• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manoman Doya 100 A Jihar Nasarawa Suka Amfana Da Horon Cibiyar NEPC

byAbubakar Abba
2 years ago
Doya

Kimanin manona 100 ne suka amfana da horon da  Cibiyar da ke kula da fitar da amfanin gona zuwa kasar waje NEPC ta gudanar  a karamar Obi da ke a jihar  Nasarawa.

An horas da manoman ne, kan dabarun zamani kan yadda za su fitar da Doyar da suka noma zuwa ketare.

  • Masanin Tattalin Arziki: Kasar Sin Ce Karfin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
  • Kasa Da Wata Biyu Ya Bar Mulki, Shin Ko Buhari Ya Cika Wa ‘Yan Nijeriya Alkawarin Da Ya Yi Mu Su?

Jami’ar  hukumar da ke a ofishin karamar Cibiyar Lafia a cikin Amina Abdullahi Tumba ce ta kadamar da bayar da horon.

Horon na kwana daya, an bude shine a shalkwatar Agyaragu, sa ke a gundumar raya karkara ta  Jenkwe da ke a cikin jihar.

Aminca a hawabinta a wajen horon ta bayyana cewa, manufar horon da aka shirya wa manoman na Doyar a jihar ta Nasarawa, an shirya masu ne domin su zamo akan gaba a daukacin fadin kasar nan wajen yin noman na Doyar.

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

A cewar Amina, jihar ta Nasarawa ta kasance ta na da kyakyawar kasa mai albarka wajen yin noma

Jami’ar ta kuma yi kira ga manoman na Doyar da suka amfana da dabarun  horon na noman na zamani lokacin horon su kara bunkasa nomansu na Doyar.

A kasidar da ya gabatar a wajen horon wani kwarare a fannin aikin noma William Akaamaa ya yi kira ga manoman na Doyar da ke a cikin jihar, da su dinga tuntubar kwararru a fannin aikin naoma ako da yaushe, musamman domin su kara habaka noman na sun a Doyar, da kuma aminta da ita a kasuwannin duniya.

A na sa bangaren Daraktan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna NAFDAC reshen jihar Babatunji Omoyeri yay i jawabi ne akan mahimancin da ke tattare da fitar da amfanin gona zuwa kasuwanin duniya domin sayarwa

Babatunji  ya kuma shawarci manoman da su tabatar da suna bin dukkan ka’idojin da aka gindaya na fitar da Doyar da suka noma zuwa kasuwar duniya, musamna domin kar a dinga kin amincewa da ita idan an fitar da ita wajen.

Shi ma a na sa jawabin a gurin bayar da horon kwamishinan aikin noma da albarkatun Ruwa na jihar Nuhu Ibrahim Oshafu, godewa Cibiyar ta NEPC ya yi kan shiryawa manoman na Doyar horon.

Oshafu ya kuma bai wa Cibiyar tabbacin cewa, gwamnatin jihar a shirye take ta yi hadaka da Cibiyar, domin a kara bayar da kwarin guiwa wajen kara bunkasa noma a jihar musaman, ba wai noman  Doya kawai ba, har da sauran amfanin gona.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
An Hana ‘Yan Jarida Shiga Wajen Tattara Sakamakon Zabe A Adamawa

An Hana 'Yan Jarida Shiga Wajen Tattara Sakamakon Zabe A Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version