Wani manomi mai suna Malam Kabiru Kamba ya bayar da labarin yadda ya ceto wata jaririya da aka haifa tare da binne ta da ranta a gonarsa da ke Kamba, a karamar hukumar Dandi a Jihar Kebbi.
Ya bayar da wannan labari ne a ranar Litinin, lokacin da tawagar ƙungiyar da ke yaƙi da cin zarafin mata da yara (GBV) ta jihar ta kai masa ziyara a gidansa.
- Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC
- Jarumin Matashi Ya Ragargaji Wani Ɗan Fashi A Kano
Kabiru ya ce ya je gonarsa ne a ranar Juma’a, sai ya ga ƙasar wani ɓangare na gonar ta bambamta.
Saboda mamakin lamarin, sai ya roƙi wasu masu babur da ke wucewa su taimaka masa ya tona wajen.
Yayin da suke tona ƙasar wajen, sai suka ga wani yadi a ciki.
Wannan ya tayar da masa hankali, sai ya kira ‘yansanda da ke kusa da wajen.
Bayan ‘yansanda sun zo sun tono ƙasar sosai, sai suka gano wata jaririya raye tana kuka, a naɗe cikin wani yadi.
Kabiru ya ce gwamnatin ƙaramar hukumar ta ba shi damar kula da jaririyar har sai ‘yansanda sun kammala bincike.
“Na yanke shawarar kula da jaririyar ne saboda jin-Æ™ai da imani da É—an Adam. Matata ma kwanan nan ta haihu, don haka za ta shayar da jaririyar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa za su raɗa wa jaririyar suna a ranar Laraba, kuma ya riga ya sayi rago da sauran kayayyakin buƙatar suna.
Matarsa ta ce ta ji daɗi kuma za ta karɓi jaririyar hannu biyu.
A lokacin ziyarar, Hajiya Rafa’atu Hammani, tsohuwar sakatariyar dindindin ta jihar, ta ce za ta kai rahoton lamarin ga matar gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Zainab-Nasare Idris.
Sakataren ƙungiyar GBV, Alhaji Nasiru Idris, ya ce sun kai ziyarar ne domin nuna gode wa Kabiru saboda ceton rayuwar jaririyar, da kuma gode wa Allah.
Ya kuma yaba wa ‘yansanda saboda saurin ɗaukar mataki, tare da alƙawarin cewa za su ci gaba da tallafa wa jaririyar.
Tawagar ta bai wa jaririyar kayayyaki kamar su sabulai, kayan jarirai, madarar jarirai, katifa, gado, da kuma gidan sauro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp