• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manufar Amurka Ta “Monroe Doctrine” Ba Za Ta Samu Karbuwa Ba

by CMG Hausa
3 years ago
Amurka

“Wannan taron kolin kasashen nahiyar Amurka, mai yiwuwa wata alama ce dake nuna raunin tasirin shugabancin Amurka a yankin Latin Amurka.” Wata kafar yada labaran kasar Mexico ce ta yi wannan sharhin.

Taron kolin kasashen nahiyar Amurka karo na tara wanda aka tsara gudanawar a birnin Los Angeles a yau Litinin 6 ga watan Yuni, sai dai kuma yadda shugabannin kasashen yankunan Amurka da dama suka yi suka tare da yin kiraye kirayen kauracewa halartar taron, da kuma matakin karshe da Amurka ta dauka na kin gayyatar kasashe kamar su Cuba, Venezuela da Nicaragua zuwa taron, duka wasu alamu ne dake nuna cewa taron kolin shiyyar wanda Amurka ke jagoranta zai iya kasancewa a matsayin wata tattaunawa ce marar fa’ida.

Tun da jimawa, shugabannin Mexico, da Bolivia, da sauran kasashe, sun taba bayyana cewa, muddin Amurka ta gaza gayyatar dukkan shugabannin kasashen nahiyar Amurkan, to su ma ba za su amsa gayyatar halartar taron kolin ba.

Kasashen yankin Latin Amurka sun gabatar da tambaya dake cewa, shin ko Amurka tana son shirya “taron kolin kasashen nahiyar Amurka ne” ko kuma “taron kolin kasar Amurka”?

A watan Nuwamban 2013, a yayin da sakataren harkokin wajen Amurka na wancan lokacin John Kerry, ya gabatar da jawabi a taron kungiyar hada kan kasashen nahiyar Amurka, yayi ikirarin cewa, “zamanin manufar Amurka ta Monroe Doctrine ya zo karshe” , kuma ya kamata kasar Amurka ta yi la’akari da kasashen yankin Latin Amurka “a matsayin abokan hulda na daidai wa daida”. Sai dai, da alama hakan bai sauya komai ba.

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

A wannan lokaci, kasar Amurka tana amfani da wannan damar karbar bakuncin taron kolin kasashen nahiyar Amurkan domin kawar da “bijirewar” da take fuskanta daga wasu bangarorin kasashen Latin Amurka, wanda wannan shi ne misali na baya bayan nan dake nuna har yanzu Amurkar tana rike da manufar “Monroe Doctrine” a matsayin tunaninta.(Ahmad Fagam)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Next Post
Bangaren Ilimi A Nijeriya Ya Tabarbare —Uwargidan El-Rufa’i

Bangaren Ilimi A Nijeriya Ya Tabarbare —Uwargidan El-Rufa'i

LABARAI MASU NASABA

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

Abin Da Ya Sa Aka Yi Watsi Da Tashar Jiragen Ruwa Ta Kan Tudu Da Ke Jihar Kaduna

October 26, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Haɗa Baki Da ‘Yan Bindiga A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwamnatin Kaduna Tare Da  AUDA–NEPAD Sun Tallafa Wa Manoma 400 Da Kayan Noma

October 26, 2025
Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru

October 26, 2025
Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu

October 26, 2025
An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.