Bayan a jiya Litinin mahukuntan yankin Taiwan na kasar Sin sun yi wani biki na wai “rantsar da shugaban yankin”, kasa da kasa sun fito karara ta mabambantan hanyoyi, wajen bayyana goyon bayansu ga manufar Sin daya Tak a duniya, wanda ke tabbatar da cewa, ba sa goyon bayan ‘yancin kan yankin.
Kasancewar Gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin a matsayin halastacciyar gwamnati dake wakiltar daukacin kasar Sin, ba sabon abu ba ne, kuma kuduri ne na MDD wanda kasa da kasa suka amince da shi. Sai dai, duk da yadda kasashen duniya ke kara goyon bayan kudurin da kuma yanke huldar jakandanci da yankin Taiwan domin kulla hulda da kasar Sin, akwai wasu ‘yan tsiraru dake yin wasu furuci ko aiwatar da wasu abubuwa dake keta wannan manufa, kuma hakan daidai ya keta dokokin kasa da kasa.
- Sassa Daban Daban Na Mutunta “Ka’idar Sin Daya Tak a Duniya” Da Adawa Da Ballewar Yankin Taiwan
- Sin Ta Bayyana Takaici Game Da Yadda Kwamitin Tsaron MDD Ya Gaza Zartas Da Kudurin Tsaron Sararin Samaniya
Gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin ta riga ta bayyana cewa, yankin Taiwan, wani bangarenta ne da ba za ta taba lamuntar ballewarsa ba. Kalubalantar wannan matsaya ta kowacce fuska, tamkar neman tada rikici ne a kasar Sin. haka kuma, keta ikon kasar ne na mallakar yankunanta.
Yadda kasashe a baya-bayan nan suke kara jaddada goyon bayansu ga manufar kasar Sin daya tak, wata zaburarwa ce ga ‘yan awaren yankin Taiwan, da ma ‘yan tsirarun kasashen dake goya musu baya cewa, su rungumi zaman lafiya, su martaba kudurin MDD da dokokin kasa da kasa, domin yunkurinsu ba zai yi tasiri ba. Haka kuma, aniyarsu ta neman tada hankalin kasar Sin ba za ta tabbata ba, domin burinta na ganin dinkewar daukacin yankunan kasar, na bisa turba, kuma abu ne da kowacce kasar da ta san ciwonta za ta yi. Lokaci ya yi da ya kamata masu ingiza ‘yan awaren Taiwan su san cewa, kasar Sin ba za ta nade hannu ta na kallo a tayar da hargitsi a kasar ba, domin ta sha nanata cewa ba za ta yi kasa a gwiwa wajen kare halaltattun hakkoki da marudu da kuma yankunanta ba, kuma wannan matsaya, ita ce daukacin al’ummar duniya ke goyawa baya.