Ga duk mai bibiyar harkokin da suka shafi kasar Sin sau da kafa, ba zai mance da yadda a yayin tarukan majalissar wakilan jama’ar kasar na NPC da majalissar bayar da shawara kan harkokin siyasa ta kasar CPPCC na bana, aka kaddamar da matakai daban daban na gyaran fuska ga manufofin kasar da suka shafi zamanantarwa irin ta Sin, tare da dora tubulin gina kasa a matakai na gaba.
A idanunmu da muke nazartar hakan, kasar Sin na ta haye tarin kalubale, a kan turbarta ta bunkasa tattalin arziki, da kyautata zamantakewar al’umma da kare hakkokin bil Adama.
- Wa Ke Dandana Kudar Matakin Harajin Kwastan Da Gwamnatin Amurka Ta Dauka
- El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC
Idan mun waiwayi baya, za mu ga yadda a watan Mayun shekarar 2023, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a kara mayar da hankali sosai ga batun daidaita bunkasar yawan al’ummar kasar Sin da ingancin rayuwarsu bisa babban matsayi. Har ma ya jaddada bukatar hade fannonin zuba jari don samar da ababen more rayuwa da tabbatar da ribar gina al’umma a bayyane. Kuma a wannan shekara mun sake ganin bayyanar wannan manufa a zahiri, cikin rahoton aikin gwamnatin kasar Sin, wanda ya fayyace matukar bukatar samar da karin kudade da hidimomi domin cin gajiyar al’umma, matakin dake kara tabbatar da matsayin kasar Sin na mai kare hakkokin al’umma ta hanyar mayar da su gaban komai.
Karkashin haka, kasar Sin ta tanadi tsare-tsare daban daban na kyautatawa al’umma, da suka hada da kyautata samar da guraben ayyukan yi mafiya dacewa da al’umma, da fadada bangarorin inshora ga ma’aikata, da saukaka damar samun nauo’in inshorar lafiya ga mazauna karkara, da mazauna birane da ba sa aiki, da rangwame kan hidimomin lafiya ga al’ummar kasa da sauran su.
Ko shakka babu a wannan zamani da neman tabbatuwar zaman lafiya, da ci gaba, da kare hakkin bil Adama suka zama burikan dukkanin sassan kasa da kasa, ma iya cewa kasar Sin ta ciri tuta, bisa kwazonta na neman hadin kan dukkanin kasashen duniya, ta yadda za a kai ga gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama, tun daga kan batun yaki da talauci, da wanzar da zaman lafiya, zuwa shawo kan kalubalen sauyin yanayi, da magance matsalolin kiwon lafiya dake addabar al’ummun duniya baki daya.
Wannan hazaka, da hangen nesa na kasar Sin, sun ci gaba da zama ginshiki na ingiza jagorancin dukkanin manufofin kare hakkin bil Adama a duniya, kana hakan zai ci gaba da zama muhimmiyar gudummawar kasar Sin ga duniya, a bangaren kare hakkin rayuwa da walwalar daukacin al’ummar duniya.(Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp