A shekarar 2023, an gamu da sauye-sauye da tashe-tashen hankula da dama, kamar rikicin da ya barke a tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, da tsakanin Isra’ila da Falesdinu. Haka kuma annobar cutar numfashi ta COVID-19 da ta barke ta yi tasiri matuka ga tattalin arziki da zaman rayuwar al’ummar kasashen duniya a shekarar 2023. Mutane na ganin cewa, mun fuskanci manyan sauye-sauye da ba a taba ganin irinsu ba a duniyarmu. A sa’i daya kuma, a shekarar 2023 da ta wuce, al’ummar kasashen duniya sun ci gaba da yin kokari domin shimfida zaman lafiya, da neman ci gaba, da yin hadin gwiwa, da kuma cimma moriyar juna. Al’ummomin kasashen duniya sun ga yadda kasar Sin ta dukufa wajen inganta harkokin zamanintar da kasa, da yadda kasar Sin ta samar wa kasashen duniya sabbin damammaki da ba da tallafi ga jama’ar kasa da kasa a lokacin da take kokarin samun bunkasuwar tattalin arziki mai inganci. Kana, jama’ar kasashen duniya sun kara fahimtar shawarar “Ziri daya da hanya daya” da kuma dalilan da suka sa shawarar ta samu karbuwa daga bangarori daban daban na duniyarmu. Haka zalika, mutane sun ga muhimmin tasirin da sabon daftarin tafiyar da harkokin kasashen duniya da kasar Sin ta gabatar ya yi wa gamayyar kasa da kasa. Wannan ya sa, a karshen shekarar 2023, wakilan Babban Gidan Rediyo da Talabijin na Kasar Sin wato CMG suka zanta da ’yan siyasa da ’yan kasuwa da kuma kwararru a fannoni daban daban daga kasar Sin da ma kasashen waje, inda suka yaba wa kasar Sin game da kokarin da ta yi a fannoni daban daban a shekarar 2023.
A shekarar 2023, kasar Sin ta sami gagarumin ci gaba a fannin zamanintar da kasa. Kwararru da shugabannin kamfanoni da dama na kasashen duniya sun bayyana cewa, abu mai muhimmanci da zai taimaka mana wajen kara fahimtar kasar Sin, shi ne dabaru da manufofin kasar Sin ta fuskar zamanintar da kasa, da gane muhimmiyar ma’anar aiki ga kasa da kasa.
- Manzon Musamman Na Shugaban Sin Zai Halarci Taron Koli Karo Na 19 Na Kungiyar Kasashe ‘Yan Ba-Ruwanmu
- Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Da Su Goyi Bayan Kasashen Yammacin Afirka Da Na Sahel
Shugaban asusun kula da dangantakar dake tsakanin kasar Amurka da kasar Sin na George H. W. Bush, Neil Bush ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta kware sosai wajen tsara shiri na dogon lokaci domin ba da jagoranci kan ayyukan neman ci gaba mai inganci. Ya ba da misali cewa, aikin zamanintar da kasar Sin ya mai da hankali kan yadda za a nemi bunkasuwa ta hanyar kare muhalli, don haka, gwamnatin tsakiyar kasar Sin da ma gwamnatocin sassan kasar sun tsara wani cikakken shirin neman bunkasuwa, inda suka ba da jagorancin raya fasahohin samar da makamashi masu tsabta, kamar amfani da hasken rana da karfin iska da sauransu, abin da ya sanya kasar zama a kan gaba a duniya a fannin nazarin fasahohin samar da motoci masu aiki da wutar lantarki.
Kamar yadda Neil Bush ya bayyana, a shekarar 2023, sana’o’in kere-kere masu amfani da fasahohin zamani kamar sana’ar sarrafa motoci sun bunkasa cikin sauri sosai, inda kasar Sin ta zarce kasar Japan a fannin fitar da motoci zuwa kasashen waje, lamarin da ya sa kasar Sin ta kasance ta farko a fannin sayar da motoci zuwa kasashen waje a fadin duniya. Kana, bunkasuwar aikin samar da motoci masu amfani da wutar lantarki ya zama daya daga cikin bangarorin da suka nuna bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin mai inganci. A shekarar 2023 da ta wuce, kasar Sin ta cimma nasarori da dama a fannin zamanintar da kasa, kamar samar da wayar salula masu amfani da fasahar IC kirar kasar Sin, da babban jiragen ruwan fasinjoji na farko da kasar Sin ta kera, da kuma samar da kumbon zirga-zirgar sararin samaniya da sauran harkokin da kasar Sin ba ta kware sosai ba a baya. Kuma, kasar Sin ta kai matsayin farko a fannonin raya fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam AI da fasahohin na’urar kididdiga ta Quantum da sauran sabbin fasahohi.
Zamanintarwa iri na kasar Sin, ba kawai za ta tallafa wa kasar Sin ba, har ma za ta tallafa wa kasashen duniya. Shugaban reshen kamfanin Shiseido dake kasar Sin Umetsu Toshinobu ya bayyana cewa, hanyar da kasar Sin take bi wajen neman bunkasuwar tattalin arziki mai inganci, ta taimakawa jama’ar kasa wajen yin kirkire-kirkire, da samar da sabbin damammaki ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. A matsayinsa na kamfani mallakin kasar waje dake kasar Sin, kamfanin zai kuma ci gaba da amfana da zamanintarwar kasar Sin.
Masanin cibiyar kwararru ta Taihe Liu Yangsheng ya bayyana cewa, masana’antun kere-kere na kasar dake kan gaba suna da muhimmanci a fannin raya tattalin arzikin kasar Sin, suna kuma ba da gudummawa a fannin raya kasashe masu tasowa dake duniyarmu. Ya ce, a halin yanzu, akwai karin kasashen duniya dake koyon fasahohin kasar Sin wajen zamanintar da kasashensu, sabo da hanyar zamanintar da kasa ta sa kasar ta cimma nasarori. Kasar Sin na neman zamanintar da kanta bisa manyan tsare-tsare, lamarin da ya nuna hagen nesan kasar Sin da kuma yadda ta tsara shiri mai inganci, kamar sabunta ababen more rayuwa da dai sauransu. Hakan ya taiamakwa jama’ar kasar Sin wajen kafa wani cikakken tsarin samarwa da fitar da kayayyaki, wanda ya kasance mafi inganci a tarihin bil Adama.
A shekarar 2023 ne aka cika shekaru 10 da gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”. Shahararren masanin harkokin kasashen duniya na kasar Iran, kana shehun malami a jami’ar Tehran Seyed Mohammad Marandi ya bayyana cewa, tun bayan gabatar da shawarar “Ziri daya da hanya daya”, shekaru goma da suka wuce, cinikayyar dake tsakanin kasashen duniya cikin wadannan shekaru 10 ta sauya sosai, wasu kasashe sun rage dogaron da suke yi kan sufurin hajoji ta hanyoyin teku sakamakon bude hanyoyin jiragen kasa a tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, matsayin kasashen dake yankin tsakiyar Asiya ya dagu sosai, lamarin da ya samar da tallafi ga wasu kasashe ciki har da kasar Iran da ma kasar Sin.
A shekarar 2023, an gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasashen duniya bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya” karo na uku a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A yayin taron da ya samu mahalarta daga kasashe guda 151 da kungiyoyin kasa da kasa guda 41, an cimma sakamako guda 458, lamarin da ya nuna kwarin gwiwar kasashen duniya wajen gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa, da babban tasirin da shawarar ta kawowa kasashen duniya.
A yayin bikin bude taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin ta fitar da manyan matakai guda 8 domin gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa kamar yadda ake fata, inda ta ba da jagora ga ci gaban ayyukan da abin ya shafa cikin shekaru 10 masu zuwa.
A matsayin muhimmin mataki cikin wadannan manyan matakai guda 8, shirin tallafawa al’umma mai taken “kanana kuma da kyau” da wasu muhimman harkokin gine-gine za su kara karfin kasashen da shawarar “Ziri daya da hanya daya” ta shafa wajen inganta hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata.
Mataimakin shugaban kwalejin nazarin shawarar “Ziri daya da hanya daya” da tafiyar da harkokin duniya na jami’ar Fudan dake birnin Shanghai na kasar Sin, Huang Renwei ya bayyana cewa, kananan shirye-shiryen tallafawa jama’a guda 1000 da kasar Sin ta yi alkawarin aiwatarwa, za su taimaka wajen raya kasuwanni, da shigar da Karin kamfanoni da hukumomi cikin shirin tallafawa al’umma mai taken “kanana kuma da kyau”, harkar da za ta kasance abin koyi cikin ayyukan gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” cikin hadin gwiwa. Sabo muhimmancin matakin aiwatar da shirye-shiryen da aka tsara bisa shawarar, lamarin zai yi muhimmin tasiri ga kasashen da suka yi hadin gwiwar gina shawarar “Ziri daya da hanya daya” cikin shekaru 10 masu zuwa.
Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana, makomar kasar Sin da ta dukkanin bil Adama a hade suke. Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen habaka moriyar bai daya dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, da samar da sabbin damammaki da kwarin gwiwa ga kasashen duniya bisa sabuwar bunkasuwar da ta samu. Kasar Sin na sa ran karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, domin zamanintar da kasashen duniya baki daya, ta yadda za a samu ci gaba cikin lumana da yin hadin gwiwa da cimma moriyar juna, da kuma samun wadata tare. (Maryam Yang)