• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Amfanin Gona Biyar Da Ya Kyautu Manoma Su Zuba Hannun Jari A 2025

byAbubakar Abba
6 months ago
Gona

Kwararru sun bayyana fannin aikin noma na kasar nan, a matsayin wanda zai bayar da wata karin dama ga masu zuba hannun jari a 2025. Daya daga cikin kwararrun, Samuel Organde ya jaddda muhimmancin cewa, fannin bai kamata ya ci gaba da kasancewa, a matsayin na gargajiya ba.

Ya sanar da cewa, maimakon haka; kamata ya yi a zuba hannun jari mai yawan gaske, musamman duba da cewa; fannin zai kara bunkasa rayuwar matasa tare da samun nasarar wanzar da sana’oi.

  • Me Sabon Karfin Samar Da Ci Gaban Ayyukan Gona Zai Kawo Mana?
  • Ministan Noma Na Gambiya: Hadin Kan Gambiya Da Sin A Fannin Aikin Gona Ya Haifar Da Sakamako Mai Kyau

Shi ma, wani kwararre Adebayo T. Adeleke, kokawa ya yi kan yadda Nijeriya ke kashe biliyoyin Nairori wajen shigo da amfanin gona daga ketare duk kuwa da irin ingantacciyar kasar noman da kasar ke da ita.

Har ila yau, Shugaban Bankin Bunkasa Aikin Noma a Nahiyar Afirka (AfDB), Akinwumi Adesina ya yi hasashen cewa; samar da abinci da kasuwar sayar da kayan amfanin gona, za ta kai dala tiriliyan daya nan da 2030, wanda kuma hakan zai sanya a kara samun zuba hannun jarin da zai kai akalla na dala biliyan 170.

Adesina ya yi kira ga masu zuba hannun jarin, da su yi amfani da damar ta samar da abinci da kuma fannin na aikin noma a Nahiyar ta Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara:

1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya

Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma wanda ake samarwa a cikin kasar, ya ragu da tan miliyan 1.4.

Kazalika, a gonar da ake noman Kwakwar Manja, za a iya samar da tan 12.5 a kowace hekta daya a duk shekara. Misali, a 2023 a heckta 20 a cikin shekara daya, an girbe Kwakwar da ta kai kimanin tan 250, inda akalla aka samu ribar kimanin Naira 150,000 na kowanne tan daya, wanda kuma ke nuna karin samun kudin shigar da ya kai Naira miliyan 37.5.

Hakan ya kuma kara nuna yadda aka kara bunkasa samun kudin shiga a shekarar da kimanin Naira miliyan 26.25.

2- Gonar  Noman Filanten:

Nijeriya ce kan gaba a duniya wajen noman Filanten, duba da cewa; a duk shekara ana noma amfanin da ya kai kimanin tan miliyan 2.8 zuwa tan miliyan 3.1.

Idan kana da Naira miliyan 5, za ka iya mallakar hekta ta noman Filanten, amma ya danganta da inda gonar taka take.

Haka zalika, bisa bai wa gonar kulawar da ta kamata, a tushe daya na Filanten a shekara, za a iya samar kimanin rassa 10,000.

Sannan, duk Nono daya na Filanten, ana sayar da shi daga Naira 2,000 zuwa Naira 4,000, inda a shekara daya, za a iya tara sama da Naira miliyan 40, wato tun daga wata 18 da aka shuka Irin nata.

Kulawar da ake ba shi a shekara bayan an shuka Irinsa, har zuwa girmansa da fara nunarsa, an kiyasata ana kashe sama da Naira miliyan 2, inda manoman za su iya samun ribar sama da miliyan 18 ko fiye da haka a shekara daya.

3- Gonar  Noman Dabino:

Nijeriya ce kan a gaba a Afirka wajen noman Dabino, duba da cewa; an kiyasta cewa, a shekara daya ana noma sama da tan 250,000.

Sai dai, abin takaici a 2024, Nijeriya ta shigo da Dabino daga ketare da ya kai na dala miliyan 17.8, inda kasar kuma ta fitar da Dabinon na kimanin dala miliyan 2,070 kacal.

Amfanin da ake yi da shi a duniya a shekara daya, ya kai akalla na tan miliyan 8.5, inda a gabas ta tsakiya da Afirka ta tsakiya, suka kasance kan gaba wajen nomansa da kuma rabar da shi.

Dabino na kaiwa tsawon shekara biyar kafin ya fara yin ‘ya’ya.

4- Irin Kwaka Na Malesiya:

A cewar wasu bayanai da Hukumar Kula da Samar da Abinci da Aikin Gona ta Duniya (FAO) ta fitar, ta dora Nijeriya kan mataki na 18 wajen noman Kwaka a duniya, duba da cewa; kasar na noma Kwakawar da ta kai kimanin tan 225,526 2021.

Wanda ya zuba hannun jari a fannin, zai  iya samun ribar sama da Naira miliyan 36 daga hekta goma da aka noma. Samar da heckta 10 a gonar noman Kwaka, zai kasance daidai da zuba hannun jari na kimanin Naira 26,550,000.

Idan har aka shuka ta, a kowace bishiya daya a shekara za ta iya samar da ‘ya’ya 100 , inda za su kai yawan ‘ya’ya 70 da za a girbe a shekara guda.

Kowane Nono daya na Kwakawar, za a iya sayar da shi kan Naira 900, wanda kuma za a iya samar da kudin shiga kimanin Naira  63,000,000 a shekara daya.

Kazalika, bayan ware kudin aikin da manomi ya kashe, zai kuma iya samun ribar da ta kai ta Naira 36,450,000 a shekara daya.

5- Gonar Noman Kashu:

A cewar wani rahoto da jaridar ‘The Nation’ ta wallafa, sama da hecta 600,000 aka ware domin nomansa, wanda zai iya samar da kimanin tan 220,000 a shekara. Farashin Kashu, ya kai daga tan Naira miliyan daya zuwa Naira miliyan 1.5.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
Noma Da Kiwo

Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina

October 3, 2025
Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo
Noma Da Kiwo

Hikimar Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoman Jihar Edo

October 3, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Kiwon Kifi

September 27, 2025
Next Post
Gwamna Abba Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Jarumi Karkuzu

Gwamna Abba Ya Yi Ta'aziyyar Rasuwar Jarumi Karkuzu

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version