ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, June 24, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Sabon Karfin Samar Da Ci Gaban Ayyukan Gona Zai Kawo Mana?

by Sulaiman
1 year ago
Gona

Lokacin bazara lokacin aikin gona ne a kasar Sin. Yanzu haka a nan kasar, manoma na fama da ayyuka a cikin gonakinsu, tare da fatan ganin samun girbi mai armashi. Sai dai abin da ya fi jan hankali shi ne yadda suke amfani da kimiyya da fasahohin zamani wajen gudanar da ayyukansu. Misali a lardin Jiangxi da ke kudancin kasar Sin, injunan gona na zamani na samun karbuwa sosai, musamman ma injin dashen tsiron shinkafa marar matuki, wanda ke iya sarrafa kansa wajen dashen tsiron shinkafa bisa taswirar gonaki da tauraron dan Adam na Beidou ya samar masa. Sai kuma a lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin, ana amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI wajen tantance yanayin gonaki tare da ba da jagorancin gudanar da aikin gona. 

A hakika, hakan ya faru ne sakamakon yadda kasar Sin ke ba ayyukan gona matukar muhimmanci. A farkon kowace shekara, takardar farko da kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta kan bayar dangane da muhimmiyar alkiblarta kusan ta kan shafi ayyuka masu alaka da gona da kauyuka da ma manoma. Ga shi a kwanan nan, an fitar da takardar ta bana, wadda ta tsara ayyukan da za a gudanar, hakan kuma, shekaru 22 a jere ke nan da takardar ke mai da batutuwan noma da kauyuka da manoma a matsayin jigonta.

  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Duba Ƙarin Farashin Wutar Lantarki
  • Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Zaftare Albashin Ma’aikata

Abin lura shi ne, a karo na farko, takardar ta bana ta gabatar da manufar “raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona”, wadda ta tsara ayyukan da za a gudanar a fannonin nazarin irrai da inganta injunan gona da kuma bunkasa ayyukan gona na zamani. Lallai “raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona” na nufin amfani da kimiyya da fasahohin zamani wajen gudanar da ayyukan gona. A kasar Sin, ya zama dole a bunkasa ayyukan gona na zamani don samar da isasshen abinci ga al’ummar kasar da yawansu ya kai biliyan 1.4, musamman a yayin da ake fuskantar matsalolin karancin gonaki da kuma raguwar yawan manoma.

ADVERTISEMENT

Raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona, ba kawai yana da ma’ana ga zamanantar da ayyukan gona a kasar Sin ba, haka kuma zai iya ba da muhimmin taimako ga kasashen Afirka wajen daidaita matsalolin abinci da talauci da ma zamanantar da kan su. A halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya na kara fuskantar matsalar samar da isasshen abinci, sakamakon matsalolin sauyin yanayin duniya da ma rikice-rikicen da ke faruwa. Ta hanyar raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona, kasashen Afirka za su iya kyautata kwarewarsu wajen samar da hatsi, tare da rage dogaro da shigar da abinci daga ketare, hakan zai taimaka ga tabbatar da samar da isasshen abinci. Ban da haka, raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona zai taimaka ga saukaka fatara a kasashen Afirka. Kasancewar sama da kaso 70% na al’ummar kasashen Afirka, musamman ma kasashen da ke kudu da hamadar Sahara, suna sana’o’i masu alaka da ayyukan gona, inganta ayyukan gona da kuma kara kudin shigar manoma na da matukar muhimmanci wajen daidaita matsalar talauci. Daga karshe, noma ya kasance ginshikin tattalin arziki a akasarin kasashen Afirka, don haka, raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona zai iya inganta ayyukan noma, wanda hakan zai sa kaimin bunkasuwar tattalin arziki baki daya.

Har kullum, noma wani muhimmin fanni ne na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. A ‘yan shekarun baya, hadin gwiwar ayyukan noma a tsakanin Sin da kasashen Afirka ya kara inganta bisa shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” da ma tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka. Tuni kasar Sin ta kafa cibiyoyin nune-nunen fasahohin noma 24 a kasashen Afirka, tare da yayata fasahohin noma na zamani fiye da 300, matakan da suka sa amfanin gonar da aka samar a yankunan da abin ya shafa karuwa da kaso 30% zuwa 60%, wadanda kuma suka samar da alfanu ga manoma na magidanta sama da miliyan 1 a Afirka. A gun taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka da ya gudana a watan Satumban bara a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da wasu matakai 10 na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wajen zamanantar da kansu, ciki har da matakin da ya shafi bunkasa ayyukan noma, kuma abin lura shi ne za a kafa kawancen kirkire-kirkiren fasahohin noma a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

LABARAI MASU NASABA

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Sin Na Daukar hakikanan Matakan Gina Kyakkaywar Makomar Al’ummun Sin Da Afirka Ta Bai Daya

Akwai makoma mai haske wajen raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona, wanda tabbas zai taimaka wa Sin da kasashen Afirka wajen gaggauta zamanantar da ayyukan gona, har ma da zamanantar da kasashensu baki daya.

Gona
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace
  • Sulaiman
    ’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin
  • Sulaiman
    Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi
  • Sulaiman
    Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

MASU ALAKA

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”
Ra'ayi Riga

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Sin Na Daukar hakikanan Matakan Gina Kyakkaywar Makomar Al’ummun Sin Da Afirka Ta Bai Daya
Ra'ayi Riga

Sin Na Daukar hakikanan Matakan Gina Kyakkaywar Makomar Al’ummun Sin Da Afirka Ta Bai Daya

June 19, 2026
A Yi Watsi Da Wannan “Mummunan Teburi”
Ra'ayi Riga

A Yi Watsi Da Wannan “Mummunan Teburi”

June 18, 2026
Next Post
NAF Ta Fara Binciken Mutuwar Farar Hula A Yayin Rikici Da Wasu Mutane A Kaduna

NAF Ta Fara Binciken Mutuwar Farar Hula A Yayin Rikici Da Wasu Mutane A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

Dokar Sin Ta Gurfanar Da Masu Rajin Ballewar Kabilun Kasar Da Ke Kasashen Waje Ta Dace

June 24, 2026
’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

’Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Sun Yaba Wa Yanayin Kasuwanci Na Sin

June 24, 2026
Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

Yadda Uba Sani Ya Farfaɗo Da Asibitin Da Aka Yi Watsi Da Shi Tsawon Shekaru 40 – Hakimin Makarfi

June 24, 2026
Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

Dandalin DAVOS Na Bana: Fage Ne Da “Kirkire-Kirkiren Sin” Ya Sadu Da “Kyakkyawan Fatan Afirka”

June 24, 2026
Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

Binciken CGTN: Amfanarwa A Aikace Shi Ne Nagartaccen Ma’aunin Tantance Ainihin Kimar Sabbin Fasahohi

June 24, 2026
Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

Kasar Sin Na Kara Zama Babban Ginshikin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya Na Gaba

June 24, 2026
Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

Tsaro: Dasuki Ya Bukaci Tinubu Ya Gyara Alaka Da Nijar Domin Kare Iyakokin Arewa-Maso-Yamma

June 24, 2026
Sabbin Ministoci

Kafa ‘Yansandan Jihohi: Majalisa Ta Amince Da Tsarin ‘Yar Tinƙe Wajen Kaɗa Ƙuri’a 

June 24, 2026
Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

Sin Ta Gabatar Da Tsarin Karfafa Kwarin Gwiwar Kamfanoni Masu Jarin Waje

June 24, 2026
Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

Shugaban Kasar Burundi: Dangantakar Afirka Da Sin Misali Ce Ta Hadin Gwiwar Kasashe Masu Tasowa

June 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.