Duk da tulin matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta, manyan bankuna gudana biyar a Nijeriya sun samu gagarumin ribar na naira tiriliyan 5.1 a shekarar 2024, wato kaso 59.4 cikin 100 daga na shekarar 2023 da aka samu naira tiriliyan 3.2.
Manyan bankuna biyar wadanda suka hada da First HoldCo, United Bank for Africa (UBA), GTCO, Access Holdings da kuma Zenith Bank, akasari sun samo ribar ne sakamakon yawan kudin ruwa da aka samu, da sake farfado da canjin kudaden waje da kuma karuwar kudaden shiga maras riba.
- An Sako Malamin Kiristan Cocin Katolika Da Aka Sace A Kaduna
- Idan Kana Son Barin PDP, Yanzu Ne Lokacin – Bukola Saraki
Baya ga haka, hada-hadar kudaden da manyan bankunan biyar suka samu ya tashi daga naira tiriliyan 9.6 a shekarar 2023 zuwa naira tiriliyan 17.3 a bara, wanda ya nuna karuwar kashi 80 cikin 100.
Bankin Zenith ya kasance a kan gaba tare da samun ribar naira tiriliyan 1.32 kafin a biya haraji, wanda hakan ke nuna karin kashi 67 cikin 100 daga naira biliyan 796 da aka samu a shekarar 2023.
Bankin GTCO ya bi sahu, inda ya fitar da ribar kashi 107.8 kafin a fara biyan haraji zuwa naira tiriliyan 1.266, daga naira biliyan 609 na bara.
Har ila yau, Access Corp da UBA sun taka rawar gani sosai, inda suka samu ribar naira biliyan 867 da kuma naira biliyan 803.7, wanda ya zarce adadin da suka samu a shekarar 2023 na naira biliyan 729 da kuma naira biliyan 757.6.
First HoldCo ya kuma samu ribar kashi 124 cikin 100 na ribar da aka samu, daga naira biliyan 347.9 a shekarar 2023 zuwa naira biliyan 781.9 a shekarar da ta gabata.
Masu gudanarwa sun yi amanar cewa juriyar da fannin banki ke nunawa ba wai kawai shaida ce ga daidaitawar cibiyoyin hada-hadar kudi ba har ma da nunin damar da za a samu nan gaba, musamman ga masu saka hannun jari da ke sa ran samun kwanciyar hankali.
Ko da yake sun bayar da hujjar cewa, idan aka yi hasashen farashin kudin ruwa zai ragu, kuma nairar za ta kara karfi tare da rage sauyin yanayi, ribar bankunan na iya fuskantar matsin lamba a bana.
Duk da haka, kwararrun sun ci gaba da jajircewa kan fannin, tare da lura da cewa bankunan da ke da kakkarfan habakar lamuni da kuma dabarun samun kudin shiga maras riba, musamman wadanda ke yin amfani da ayyukan kasuwanci, da alama za su kasance masu jan hankali ga masu zuba jari.
Wani manazarci, Charles Abuede, ya ce ayyukan bankunan Nijeriya a cikin shekara ta 2024 suna ba da manuniya mai kyau ga abin da ke gaba a 2025.
Ya ce, akwai hasashen za a samu karin tagomashi sosai a bangarorin a shekarar bana, wanda a cewarsu ayyukan na kyau matuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp