Bisa alkaluman ci gaban GDPn kasar Sin na watanni ukun farkon shekarar bana, wasu cibiyoyin hada hadar zuba jari na kasa da kasa sun daga hasashen su na ci gaban tattalin arziki da Sin din za ta iya samu a wannan shekara.
Cibiyar J.P. Morgan, ta daga hasashen ci gaban tattalin arzikin kasar Sin a bana, da karin kaso 0.4 bisa dari, inda hasashen ya tsaya kan kaso 6.4 bisa dari, yayin da bankin Citibank ke biya da na sa hasashen, wanda ya karu daga kaso 5.7 zuwa kaso 6.1 bisa dari.
Su ma bankunan Goldman Sachs da Deutsche Bank, sun daga hasashen na su ne zuwa kaso 6 bisa dari, bisa dogaro da bunkasar tattalin arzikin da Sin din ke samu a halin yanzu. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp