Bisa umarnin shugaban kasar Sin kuma sakatare janar na JKS Xi Jinping, tawagar mambobin kwamitin tsakiyar jam’iyyar sun ziyarci jami’ai da mazauna birnin Lhasa, hedkwatar jihar Xizang mai cin gashin kanta, dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Wang Huning, mamban zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar kuma shugaban majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), shi ne ya jagoranci tawagar da ta kai ziyarar a jiya Alhamis.
- Likitoci Sun Gano Wuka Da Aka Burma A Kirjin Wani Mutum Tsawon Shekara 8
- Ruben Dias Ya Rattaba Hannu Kan Sabon Kwantiragi A Manchester City
Da suka ziyarci manyan jami’ai na birnin Lhasa da wakilai daga kabilu da bangarori daban-daban, Wang Huning ya yi kira da a yi kokarin samun nasara a manyan bangarori 4, da suka hada tabbatar da kwanciyar hankali da inganta samar da ci gaba da kare muhalli da karfafa tsaron iyakoki, ta yadda za a bayar da sabbin gudunmuwa ga tabbatuwar zaman lafiya mai dorewa da kwanciyar hankali da ci gaba mai inganci a Xizang.
Da suka ziyarci wasu masu kishin kasa dake ibada a wurin bauta na Jokhang, Wang Huning ya bayyana fatan ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kare hadin kan kasa da karfafa goyon bayan juna tsakanin kabilu da shiga a dama da su cikin harkokin gina sabuwar Xizang mai tsarin gurguzu na zamani.
Tawagar ta kuma nazarci ci gaban da aka samu a fannin bayar da ilimi a jami’ar Xizang tare da ziyartar wani wurin shakatawa domin ganin kokarin da ake yi na dasa bishiyoyi da kare tsirrai a wurin. Babban jami’in na Sin ya kuma nanata bukatar mayar da hankali kan inganta rayuwar jama’a da samar da ayyukan yi da karuwar kudin shiga ga al’umma da kuma samar da wadata ta bai daya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp