Wasu kasashen yamma sun dade suna karawa batun bashin da Sin take baiwa Afrika gishiri, musamman ma bayan an gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, sun bayyana bashin da Sin take baiwa kasashen Afirka a matsayin abin da zai haifar da matsalar bashi.
Irin wannan kalamai na cewa wai bashin da Sin take baiwa Afrika tarko ne, na da nufin hana bunkasuwar hadin kan Sin da Afirka da cin moriya tare.
- Xi Ya Gana Da Firaministan Girka Da Yin Tattaunawa Da Shugaban Gwamnatin Jamus
- Baje Kolin CIIE Na Kara Jan Hankalin Sassa Kasa Da Kasa
Sinawa na da wani karin magana dake nuna cewa, idan ana son tabbatar da ganin bunkasuwar tattalin arziki, dole ne a fara ne da gina hanyoyi. Shi ya sa, rancen kudin da Sin take baiwa Najeriya wajen aiwatar da ayyukan hadin gwiwa karkashin wannan shawara ta “ziri daya da hanya daya”, yawancinsu ana amfani da su wajen samar da manyan ababen more rayuwa. Alal misali, an gina layin dogo na farko mai amfani da ma’aunin Sin a Afrika, wato layin dogo dake tsakanin Abuja da Kaduna a Najeirya, da kuma layin dogo na farko dake cikin birni a yammacin Afirka, wato layin dogo na Abuja na Najeirya.
A can baya tsohon shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya taba shaidawa manema labarai cewa, rancen kudin da Sin take baiwa Najeriya, an yi amfani da su ne wajen gina layin dogo, da hanyoyin mota da dai sauransu, kuma idan babu irin wadannan ayyuka, al’ummar kasar ba yadda za su yi sai su yi zirga-ziraga da kafafu. Ya kuma yi maraba da duk wata kasa dake iya baiwa kasarsa taimako a fannin gina manyan ababen mora rayuwa.
Amma shin me ya hana wadannan kasashen yamma?
A farkon watan bara na kai ziyara a Najeriya, na kuma zanta da kakakin majalisar wakilan tarayyar Nijeriya Abbas Tajudeen, kuma yayin zantawar mu ya ce, kasashe da dama suna shirin baiwa Najeriya rancen kudi, amma kasashen Afrika suna zabar rancen da ya dace da yanayin da suke ciki. Idan an kwatanta da manufofin sauran kasashe, rancen kudin da Sin ta samar na kunshe da kudin ruwa mai araha, da wa’adi mai tsawo. Najeriya na godiya sosai kan taimakon da Sin take ba ta wajen raya tattalin arzikinta. Ban da wannan, bisa rahotannin da wasu hukumomin kasa da kasa, da kungiyoyin nazari suka bayar, an ce, yawancin basusukan da kasashen Afirka suke karba na fitowa ne daga daidaikun mutane na kasashen yamma.
Kasashen Afrika na da ma’ auninsu na zabar abokan hadin gwiwa, bisa la’akari da moriyarsu. A halin yanzu, karin kasashe sun karbi shawarar “ziri daya da hanya daya”. Alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta dauka game da hadin gwiwar shawarar daddade ne, kuma ya dace da muradunsu, shi ya sa ta samu amincewa daga kasashe, da jama’arsu da suka karbi shawarar. Ban da wannan kuma, rancen kudin da Sin take baiwa kasashen, ana amfani da su ne wajen gina manyan ababen more rayuwa, matakin da zai ingiza bunkasuwar tattalin arzikinsu. Kaza lika idan an yi hangen nesa, za a ga cewa zai taimakawa wadannan kasashe wajen biyan bashin da kasashen yamma, da wasu hukumomin kudaden kasa da kasa suke binsu. (Mai zana da rubuta: MINA)