Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tir da kisan da ‘yan Bindiga suka yiwa Babban Malamin Cocin Catholic Diocese, John Cheitnum a Kafanchan jihar Kaduna.
Buhari ya ce, tabbatar da tsaro ga ‘yan Nijeriya shi ne babban abinda Gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai, inda ya kara nanata cewa, Gwamnatinsa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen kawo karshen hare-haren ‘yan Bindigar.
Shugaban wanda ya bayyana hakan a cikin sanarwar da mai taimaka masa a harkar yada labarai, Garba Shehu ya fitar a Abuja, ya ce, manyan jami’an tsaro na kasar nan ba za su huta ba har sai an samar da cikakken tsaro a kasar nan.
Buhari ya kuma Mika ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwa da kungiyar CAN da kuma Gwamnatin jihar Kaduna bisa kisan Malamin cocin.
An dai tsinci gawar Fada John Cheitnum ce a ranar 19 ga watan Yulin 2022.
,
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp