Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB), ta sanar da maki 140 a matsayin mafi karancin makin da zai bai wa dalibai damar shiga Jami’a a 2022.
Mafi karancin makin na makarantun polytechnic da Kwalejin Ilimi shi ne maki 100.
- Zaben Osun: INEC Ta Bai Wa Adeleke Takardar Shaidar Lashe Zabe
- Gabatar Da Shettima: Naira 100,000 Aka Yi Mana Alkawari, Amma Naira 40,000 Aka Ba Mu – Bishop
An bayyana hakan ne a wani taro da ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ya jagoranta a Abuja a yau ranar Alhamis.
Magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede a baya ya nuna mafi karancin maki da manyan makarantun za su dauki dalibai da shi ya sha bambam da na wannan shekarar.
Ba kamar shekarar 2021 ba, alamomi sun nuna cewa makarantu ma na da nasu damar na fitar da makin na 2022.
A cewarsa, jami’o’in tarayya za su kasance da kashi 45 cikin 100 yayin da jami’o’in jiha za su samu kashi mafi karanci.
Idan ban manta ba dalibai da dama sun zana jarrabawar Jamb da nufin neman gurbin shiga Jami’a ko kuma manyan makarantun gaba da sakandare