ALHAJI MUHAMMAD ADAMU MAKARFI, guda ne cikin wadanda suka yi fice a bangaren harkar noma a Arewa, har ila yau shi ne Shugaban Kungiyar Manoma-masara, domin samun riba na Arewa Maso Gabas, sannan mai yin fashin baki, a kan harkokin tattalin arziki na kasa. A tattaunawarsa da wakilinmu ABUBAKAR ABBA, ya zayyana wasu daga cikin manyan nasarori tare da kalubalen da fannin noma ya fuskanta a shekarar 2023 da sauran makamantansu.
Bari mu fara da duban manyan kalubale kafin mu kai ga nasarori. A naka ganin wadanne irin kalubale wannan fannin ya fuskanta a 2023?
Babu shakka, akwai matsaloli da dama; amma kamar yadda ka tambaye ni, wadannan manyan kalubale sun hada da rashin samun ingantaccen Irin noma, ifila’in ambaliyar ruwan sama da aka samu a wasu jihohin kasar nan kamar Jihar Zamfara, Sokkwato, Jigawa, Katsina Kaduna da kuma sauran wasu jihohi da ke Kudancin Nijeriya, wanda hakan ya yi sanadiyyar jawo wa manoma da dama yin asara.
Har ila yau, akwai batun ayyukan ta’addacci na ‘yan bindigar daji, amma duk da haka mun yi wa Allah godiya, dalili kuwa duk da faruwar hakan wasu manoma sun samu damar yin noma a gonakinsu tare da samar wa da wannan kasa abinci.
Haka zalika, mun fuskanci kalubalen tsadar takin zamani; wanda farashin duk buhu guda ya kai kimanin naira 30,000 zuwa 35,000, sannan wannan ya danganta da nau’in irin takin zamanin, wanda ko shakka babu ba karamin babban nakasu ne ga wannan fanni na aikin gona ba, musamman kananan manoman da ke karkara.
Har wa yau, an kuma fuskanci kalubalen rashin ingantaccen Iri; wanda ya kamata a rika samar da ingantaccen wannan Iri, domin manoma su rika samar da wadataccen abinci a fadin wannan kasa tare da rika fitar ta shi zuwa wasu kasuwannin duniya.
Sannan, mun kuma fuskanci rashin samun bashi daga bankunan ‘yan kasuwa, domin yin noma da rashin kayan aikin noma na zamani, kazalika mun fuskanci sauyin yanayi da kuma yadda wasu manoman musamman a karkara ba su samu amfanin gona mai yawa ba.
Bugu da kari, tallafin da gwamnatin tarayya ke bai wa manoma ta hanyar Babban Bankin Kasa (CBN), karkashin shirin aikin noma na ‘Anchor Borrowers’, ba kasafai ya ke kai wa ga ainahin manoman da ya kamata su amfana da shi ba. Haka nan, wani lokacin ana bayar da wannan tallafi ne daga watan takwas zuwa watan tara, tuni bayan manoma sun yi nisa da aiki a gonakinsu.
Haka zalika, sauya takardun kudi wanda Babban Bankin Kasa (CBN) ya yi lokacin Emefele, ya yi matukar jawo asara ga manya da kuma kananan manoma a fadin wannan kasa, wanda hakan ya haifar da hauhawan farashin kayan abinci da kuma kara farashin kayan aikin noma baki-daya.
Akwai kuma batun kalubalen cire tallafin man fetir, wanda Shugaban Kasa Tinubu ya yi, inda hakan ya haifar da tsadar sufurin jigilar amfanin gona zuwa kasuwanni da kuma tsadar sayen man, musaman ga manoman da ke shirye-shiryen fara yin noman rani.
Sannan, har yanzu manoma musamman na karkara, na fuskantar kalubalen rashin hanyoyi masu inganci, wadanda za su taimaka masu wajen jigilar amfaninsu zuwa kasuwanni, wanda hakan yasa suke sayar da amfanin a cikin gonakinsu a kuma farashi mai sauki, maimakon kai shi kasuwa su sayar da da tsada, su samu gaggwabar riba.
Akwai kuma matsalar sayar wa da manoma gurbataccen maganin feshi, musamman wadanda suke a karkara, sannan mun kuma fusantaci kalubalen rashin ingantaccen Iri da ke jurewa kowanne irin yanayi bayan an shuka shi, wanda hakan ya haifar da asara ga manoma da samar da wadataccen abinci a wannan kasa.
Haka nan, wasu ‘yan kasuwa sun bi manoma har cikin gonakinsu sun saye dukkanin amfanin gonar da suka noma a kan farashi mai sauki, ba don komai ba sai kawai domin su boye bayan ya yi tsada sannan su fito da shi. Ina mai tabbatar maka da cewa, wannan fani a wannan shekara ta 2023 ya fuskanci matsaloli iri daban-daban tare da kalubale, wanda lokaci ba zai ba mu damar bayyana baki-daya ba.
A bangaren sama wa manoma taraktoci fa, me za ka ce?
Tiraktoci sun yi karanci matuka, wadanda sanin kowa ne suna da matukar mahimmancin kaske a wannan fanni na noma, har ila yau Nijeriya na da kananan hukumomi 774, wanda ya kamata a ce kowace karamar hukuma akalla tana da taraktoci guda 1,000, domin kuwa kashi 70 cikin dari na ‘yan Nijeriya manoma ne, wanda mu a nan Arewa cewa muke yi kashi 95 na al’ummarmu manoma ne.
A 2023, wasu ‘yan Nijeriya sun dora alhakin rashin samun wadataccen abinci a kan manoma, musamman masara da ta fi zama cimaka ga talaka, me ya faru?
Mafi yawan masu fadin haka ‘yan baranda ne, domin ba da ban irin gudunmar da muke bayar wa a wannan harka ba, da tuni yunwa ta afka wa Nijeriya, dalili kuwa gwamnati ba ta da kudin da za ta iya shigo da amfanin gona daga kasashen ketare, wanda zai iya wadata Nijeriya. Shi yasa gwamnatin ta tabbatar da raya noman rani, domin a samu a cike gibin da aka rasa a noman na bana.
Tinubu ya ware wa fannin noma naira biliyan 362 a kasafin kudi na 2024, ka gamsu da wannan kasafin da aka ware?
A gaskiyar magana bisa kuduri na shugaban kasa da ya ce, ya sanya dokar ta baci a harkar noma, ya kamata a ce kudin da aka ware sun haura wannan adadi. Sannan, ya kyautu a tsaya a yi duba mai kyau tare da fayyace abubuwan da harkar noma ke bukata, wadanda kuma za su inganta harkar, musamman abin da ya shafi harkokin tsaro, wanda Tinubu ya bayar da tabbacin cewa, zai yi duk abin da ya dace domin tabbatar da shi, musamman don ganin manoma sun koma gonakinsu.
Sannan na biyu, a kudurorin da shugaban kasar ya shinfida ya bayar da tabbacin za a samar da rance kudin yin noma, musamman ga kananan manoma da ke karkara, domin bunkasa harkokin nomansu.
Har ila yau ya kuma ce, za a bunkasa harkar noman rani da kuma batun takin zamani, wanda ya zama babbar matsala ga manoma tare kuma da sama musu tallafi a-kai-a-kai. Don haka, a matsayinmu na manoma, duk inda aka ce an janye tallafin man fetur, wajibi a kawo mana tallafi a harkar noma, domin radadin da muke fuskanta ya ragu.
Misalli yadda ake sayen taki a kan naira 30,000 zuwa Naira 35,000, ya danganta da nau’in takin, ya kamata a ce an mayar mana da farashinsa kan naira 3,000 kan duk buhu guda, tun da tsohuwar gwamnatin Buhari a kan 5,000 ta kayyade masa farashi, amma wasu marasa tausayi sai suka kar farashi. Saboda haka, ya kamata Tinubu ya kara rage farashin wannan taki na zamani, yadda manoma da dama za su iya yin wannan noma.
Saboda haka, magana ta gaskiya wannan kasafi na naira biliyan 362, ya yi matukar kadan, sai dai idan zai yi wani kasafin ne na da ban; domin wadannan adadin da ya ware, babu inda za su je a wannan harka; domin kuwa masu iya magana na cewa, “noma babu taki, wahala”. Zance na Allah, wannan kaso ba zai isa ba. Koda-yake, mun ji gwamnatin tarayya ta ce za ta shigo da taraktoci, muna fatan Allah ya sa wannan kuduri nata ya wanzu.
Bara kuma mu dawo batun nasarorin da aka samu a wannan shekara ta 2023, me za ka ce?
Ko shakka babu, zan iya cewa an samu nasarori, wadanda suka hada da kirkiro da shirin inganta kiwon dabbobi; wanda Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi na ‘NLTP’, inda har a halin yanzu ake ci gbaa da wanzar da shi, domin kokarin samar da mafita a kan rikicin makiyaya da manoma.
Haka zalika, wasu jihohin sun samar da filayen da aka kafa wajen yin kiwon zamani, inda gwamnatin tarayya ta bayar da makudan kudade; domin tabbatar da shirin. Don haka, muna fatan za a ci gaba da gudanar da shirin kamar yadda aka tsara.
Har ila yau, tsohuwar gwamntin Buhari, ta amince da yarjejeniyar kasuwanci kai tsaye ta Afirka (AfCFTA), domin fitar da kaya waje ciki har da amfanin gona tare da samar da kasuwa.
Bugu da kari, bayan samun afkuwar annobar ambaliyar ruwan sama; gwamnati ta taimaka wa manoman da iftila’in ya shafi a gonakinsu.
A karshe ina mafita game da kalubalen da ka bayyana a baya?
Ya kamata a fahimci cewa, fannin noma kashi-kashi ne, don haka wajibi ne a bai wa wannan harka muhimmancin gaske tare da raya ta domin samar da abinci. Sannan, babbar mafita a nan ita ce; wajibi ne gwamnati tarayya da na jihohi su samar da kyawawan tsare-tsare tare da shirye-shirye masu dorewa, don ci gaba da habaka wannan fanni na noma.
Kazalika, gwamnati musamman ta tarayya, dole ne ta tabbatar da samar da wadatattatun kudade, domi tallafa wa manoma tare kuma da tabbatar da ganin cewa dukkanin tallafin da ta ke bayarwa ya isa ga manoma na gaskiya, ba na boge ba. Babu shakka idan aka samu hakan, wannan harka za ta bunkasa, ta kuma samar da abin da za a ciyar da kasa har a kai ga fitarwa sauran kasashen ketare.