Manyan ‘Yan Majalisar Birtaniya ciki har da Firaiminista Liz Truss sun yi mubaya’a ga Sabon Sarki Charles III a wani zama na musamman da majalisar kasar ta yi.
Kakakin Majalisar Wakilan Birtaniya, Lindsay Hoyle, ne ya bude zaman bayan yin mubaya’a, bayan nan sai kuma Sir Peter Bottomley, wanda shi ne dan majalisa da ya fi dadewa a majalisar.
Hoyle, ya bayyana cewa sakamakon karancin lokaci, ‘yan majalisa k alilan ne kawai za su iya yin mubaya’ar.
Truss na daga cikin wadanda suka yi mubaya’ar inda suka rantse cewa za su yi biyayya ga sabon sarki Charles III da magadansa kamar yadda doka ta tanada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp