Tun daga ranar 24 zuwa 25 ga wannan wata, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), Jiang Zuojun ya halarci jana’izar marigayi shugaban kasar Namibia Hage Geingob da aka gudanar a birnin Windhoek. A ranar 25 ga wata da yamma, sabon shugaban kasar Nangolo Mbumba ya gana da manzon musamman Jiang Zuojun a fadar shugaban kasar.
Jiang Zuojun ya isar da gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping ga shugaba Mbumba, tare da mika taaziyya ga rasuwar marigayi shugaba Hage Geingob, da kuma jajantawa gwamnatin kasar Namibia da jamaarta.
- Wani Sojan Amurka Ya Bankawa Kansa Wuta Don Nuna Goyon Bayansa Ga Falasdinawa
- Liverpool Ta Lashe Kofin Carabao Karo Na 10 Bayan Doke Chelsea A Wembley
A nasa bangare, shugaba Mbumba ya nuna godiyarsa ga shugaba Xi Jinping da ya tura manzon musamman zuwa kasar, kana ya jaddada cewa, kasarsa ta Namibia za ta ci gaba da yin kokari tare da kasar Sin don kara sada zumunta a tsakaninsu da amfanawa kasashen biyu da jamaarsu. (Zainab Zhang)