A ‘yan kwanakin baya ne daraktan ofishin dake lura da harkokin waje, na kwamitin kolin JKS Wang Yi, ya gabatar da shawarwarin kasar Sin, don gane da karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, yayin taro na 13 na kasashe mambobin kungiyar BRICS, taron da ya hallara mashawartan kasashe mambobin kungiyar ta fuskar tsaro, da kuma manyan wakilan kasashen a fannin na tsaro.
Da take tsokaci game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce rukunin kasashe masu tasowa, ya kunshi kasashe da tattalin arzikin su ke bunkasa cikin sauri, da sauran kasashe masu tasowa.
Jami’ar ta ce shawarwarin 4 da Sin ta gabatar, sun hada da kara azamar kawar da tashe tashen hankula, da hada karfi da karfe wajen tabbatar da zaman lafiya. Sai kuma shawara ta biyu, wadda ta shafi kara kwazon ingiza manufofin wanzar da ci gaba. Kaza lika akwai shawarar jan hankalin kasashe da su bude kofofin su, tare da yin tafiya tare da kowa domin cimma nasarori. Shawara ta 4 kuwa ta shafi matsa kaimi wajen inganta goyon bayan juna da hadin gwiwa.
Mao Ning ta jaddada cewa, Sin a shirye take ta yi aiki tare da daukacin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa cikin sauri, da sauran kasashe masu tasowa, wajen yayata aiwatar da manufofin samar da ci gaban kasa da kasa, da tsaron duniya, da manufofin wayewar kan duniya, da ma hada hannu wajen gina al’ummar duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil adama. (Saminu Alhassan)