Bisa wasu rahoatnin da kafafen yaɗa labarai suka wallafa, wasu ƴan ƙasar, sun yi hasashen cewa, ƙasar ba wai kawai na ci gaba da fuskantar matsalar tsaro ba ne.
Misali, mayaƙan ƙungiyar ƴan ta’adda ta ISWAP, a kwanan baya ta yiwa tawagar wasu dakarun soji kwanton Ɓauna a babbar hanyar Damboa, da ke a jihar Borno, inda suka kama Birgediya Janar M. Uba, da ransa, suka kuma yi masa kisan gilla.
- Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Janar Musa A Matsayin Ministan Tsaro
- Sin Da Rasha Sun Yi Shawarwari Kan Manyan Tsare-tsaren Tsaro
Hakan ya nuna cewa, waɗannan ƴan ta’addar ba wai kawai masu akita muggan laifuka na je ken a yi bane, musamman duba da cewa, su kan kasance, ɗauke da muggan makamai, a duk lokacin da za su kai hare-harensu.
Kazalika, a kwanan bayan gungun wasu ƴan bindiga sama da 30, ɗauke da muggan makamai a kan Babura, sun aukawa ƙauyen Fegin Baza na jihar Zamfara, suka hallaka mutane uku cikinsu har da wani jigo na jam’iyyar APC, tare da kuma sace wasu fararen Hula 64 da mata da kuma yara.
Wasu rahotannin sun ce, miyagun sun kai wannan harin ne, ƴan sa’oi baya tawagar kwamishinan ƴansanda na su wuce, hakan na nuna cewa, kodai dama, ƴan bindigar ba su taki sa’a bane, a lokacin harin na su ko kuma wani da masaniyar, daidai lokacin da suka tsara, kai harin na su.
Bugu da ƙarin, maharani sun kuma sake karkata akalarsu zuwa jihar Kebbi, inda suka kutsa cikin makarantar ƴan mata ta gwamnati da ke a garin Maga, suka yi awon gaba da ƴan mata 25, waɗanda wasunsu, ƴan shekaru 13 ne, tare da hallaka wani jami’in makarantar mai suna Hassan Makuku.
A yankin Arewa ta Tsakiya ma, haka batun yake, inda maharani suka kutsa cikin Cocin Christ Apostolic da ke a yankin Eruku, na jihar Kwara, suna ta faman ruwan ruwan Albarusai, ba ƙaƙƙautawa, a yayin da mahalarta Cocin, ke kan gudanar da ibada, suka hallaka aƙalla mabiya uku tare da sace Jagoran Cocin da kuma wasu mabiya.
Duk dai a jihar ta Kwara, wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu manoman Shinkafa huɗu a yankin Edu.
Hakazalika, sun kai hari a garin Sabon Birni na jihar Sokoto, suka hallaka wani Basarake tare da sace wasu mutane 15, cikinsu har da wasu mata huɗu tare da jariran da suke shayarwa.
A jihar Yobe kuwa, mayaƙan ISWAP, sun auka a wani ƙaramin ofishin ƴansanda da ke a Geidam, suka kashe ɗansanda ɗaya suka kuma bankawa wasu motocinsu na fatirol wuta.
Ita jihar Neja, ba ta sha ba, domin maharani, su aukawa makarantun St. Mary’s Catholic da ke a yankin in Agwara, suka sace ƙananan ɗalibai sama da 300 da malamai sha biyu.
Ko da yake dai, an ruwaito cewa, gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwar kafin kai harin na su ce, an samu bayanan sirri na matsalar tsaro a yankin.
A nan, za mu iya cewa, ba wai batu ne, na samun rahoton barazanar tsaro a jihar ba, amma lamari ne, kawai, da ke nuna cewa, mahukunta a Arewacin ƙasar, sun gaza wajen tsaron rayuka da dukiyoyin alummar yankin.
Wannan ƙalubalen na ƙarauwar matsalar tsaron ce, ta tilasata shugaba Bola Tinubu ya dakatar da tafiyar da ya tsara yi zuwa wani babban taro a ƙasashen Afirka ta Kudu da Angola, musamman domin jiran bayanai daga hafsjoshin tsaron ƙasar.
Tinubu, ya bayar da umarnin da a ƙara tura jami’an tsaro zuwa yankin na Eruku tare da umartarsu, da su bankaɗo duk inda miyagun suke a ɓoye.
Kazalika, ya umarci ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle, da ya tare a jihar Kebbi, har sai an gano ɗaliban da aka sace.
Tinubu ya kuma bayar da umarnin, da a rufe ɗaukacin makarantun sakantare na haɗaka 47, na ƙasar, wanda ya danganta wannan matakin saboda matslar ta tasaro.
Wannan matakin ya nuna a zahiri cewa, gwamnatin ba za ta iya kare rayukan ɗaliban ba
Tabbas, muna buƙatar a lalubo da mafita kan matsalar ta rashin tsaro, musamman duba da cewa, duk da irin yawan jami’an tsaron da ƙasar ke da su, amma gwamnatin, ta gaza kare rayukan ɗaliban.
Alamar tambayar a nan shi ne, rufe makarantun da tura ɗaliban gida shi ne mafita, bayan cewar, wasu alumomin da ɗaliban suka fito na ci gaba da fama da hare-haren ƴan bindiga?
Darun sojin mu, na mutuwa a fagen daga, ana kuma sace ɗalibai, yan bindiga na kai hare-hare a Coci-Coci, manoma a gonakansu, ba su tsira ba, manyan hanyoyi na ci gaba da zama tarkon mutuwa ga matafiya.
Ya zama wani, kar shugaba Tinubu yayi sako-sako da wannan ƙalubalen, domin akwai buƙatar ayyana dokar ta ɓaci kan lamarin.
A bisa wannan matsalar ce, ƙasar Amurka ta ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ya wajaba a mayar da hankali kan ƙalubalen rashin tsaro da rashin bai wa ƴan ƙasar ƴancin yin addini.
Wasu na yin hasashen cewa, ci gaba da samun tashe-tsahen hankula a ƙasar, na da nasaba da yunƙurin yiwa Tinubu zagon ƙasa domin kar gwamnatinsa ta wuce zuwa wa’adi na biyu.
Kazalika, akwai buƙatar a cafko waɗanda ake gani a ƙasar, sun eke ɗaukar nauyin ayyukan ta’addamci ko wanne irin matsayi na siyasa, suke riƙe da shi.
Hakazalika, akwai buƙatar a dakatar da duk wasu manyan taruka na siyasa, kuma a jingine batun duk wani lissafai, na yaya za a lashe zaɓen 2027.
Bisa wannan matsalar, tabbasa ba mu riga Malam Masallaci ba, idan muka ce, Nijeriya a yanzu, na cikin yaƙi ne kuma abin tambayar a nan shi ne, shi shugaban Tinibu, gwamnatinsa a shirye take ta fara yaƙar matsalar matsalar tsaron da ta zamo wa ƙasar ƙarfan ƙafa?














