• English
  • Business News
Saturday, November 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Maraba Da Azumin Ramadan Na Bana

by SP. Imam Ahmad Kutubi
3 years ago
Azumi

Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu. Mun Fara Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai, Dukkan Yabo Da Godiya Sun Tabbata Ga Allah Ubangijin Talikai, Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Shugabanmu Annabi Muhammad Da Iyalansa Da Sahabbansa Baki Daya.

Da farko muna wa kowa da kowa barka da shiga wannan wata mai alfarma na Azumin Ramadan. Da fatan Allah ya karbi ibadunmu, Allah ya sa muna daga cikin wadanda za a ‘yanta.

  • Zaben Gwamna: PDP Za Ta Yi Zanga-Zangar Kwana 7 Kan Sakamakon Zaben Nasarawa 
  • ‘Yan Nijeriya Sama Da Mutane 39 Ne Suka Mutu A Zaben 2023

Shi dai Azumin watan ramadana farilla ne, yana daga cikin shikashikan musuluncin nan biyar. Wanda ya yi niyyarsu tun a cikin daren farko na ramadana, niyyar nan guda ta wadatar domin azumin watan ramadana dukkansa. Idan mace ta shafa tozali tun gabanin alfijir, ko kuma mutum ya saka magani a cikin hancinsa, to ko maganin nan ya gangaro ga makogaro da rana azumi bai karye ba. Idan kuwa ya karya shi ne da gangan, ko kuwa ya di daukarsa ba da wani uzuri ba, to zai rama shi ta kowane hali, sannan kuma ya kara da yin kaffara. An halatta wa matafiyi, tafiya irin wadda ta hallata a gajarta sallah dominta, ya sha azumi, amma ya yi ramuwa. Mai itikafi ba zai fita masallaci don gai da marasa lafiya ba, sai idan dayan iyayensan ne. Kuma ba zai fita don sallah a kan mamaci ko don yin ciniki ba.

Ma’anar Azumi

Azumi shi ne kamewa daga dukkan abin da ciki da farji ko zakari suke sha’awarsa, tun daga alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada.

LABARAI MASU NASABA

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

Azumin watan ramadana farilla ne, yana daga cikin shikashikan musulunci guda biyar.

Tabbatar Tsayuwar Wata

Tsayuwar watan ramadana yana tabbata da samuwar daya daga cikin abubuwan nan biyu da za mu ambata; Ganin sabon watan ramadan da ido, a ranar da sha’aban ya cika kwana ashirin da tara. To, idan mutum biyu adalai suka ga wata da idanunsu, azumi ya wajaba ga dukan wanda ya sami labarin ganin wata. Adali shi ne wanda baya aikata manya zunubai Kuma yana kokari ga barin kananan zunubai da galib6insu.

Haka kuma kama azumi yana wajaba idan taron mutane da yawa wadanda ba adilai ba suka ce sun ga wata, alhali kuma don yawansu har ba ya yiwuwa a ce ko sun hada kai ne don su fadi karya. Amma idan mutum guda daya ne ya ga wata, ba za a kama azumi domin ganinsa shi kadai ba ko da kuwa ya fi mutanen duniya gaskiya da adalci. Amma shi wanda ya ga wata ko da ba adali ba ne wajibi ne a kansa ya dauki azumi tare da shi da iyalansa kadai, sauran mutane kuwa ba ruwansu.

Kuma wajibi ne a kan wanda duk ya ga wata ko da fasiki ne, ya je gun sarki ko shugabannin addini na garinsu ya sanar.

Idan an ga wata a wata kasa mai nisa can gabas, idan mutanen wata kasa ta yamma da su suka sami labari daga garesu, a wani kauli na malamai ya halatta su dauki azumi tare da su, a wani kauli kuma bai halatta ba sai dai idan duk malamai sun yi ittifa’ki cewa idan tsakaninsu akwai nisa kwarai bai halatta su yi koyi da su ba. Kamar tsakanin indiya da spain.

Dalili na biyu wanda zai tabbatar da tsayuwar watan ramadana shi ne cikar watan sha’aban kwana talatin cif. To, ko da ba a ga watan ramadana ba sai a yi azumi hakan.

Dalilin da aka bi don tabbar da tsayuwar watan ramadan su ne kuma za a yi aiki da su don tabbatar da tsayuwar watan shawwal. Wato watan karamar sallah.

Sharuddan Wajibcin Azumi Da Ingancinsa

 Sharuddansa Bakwai Ne (7)

Niyya: Wajibi ne mutum ya yi niyya ya ce; Nayi niyyar yin azumin watan Ramadana, farilla. Tun daga faduwar rana har zuwa fitowar alfijir duk lokaci ne na yin niyya. Amma ana fadan haka ne a cikin zuciya. Wanda ya yi niyyarsa tun a cikin daren farko na Ramadana, niyyar nan guda ta wadatar domin azumin watan Ramadana har ya gama dukkansa. Amma da sharadin kwanakin azuminsa su bi juna, ba su yanke ba. Idan ko da kwana daya ne ya baci, ko kuma bai dauki azumi a cikinsa ba don rashin lafiya, ko tafiya, ko haila ko jinin biki, to wajibi ne ya sake wata sabuwar niyya domin ragowar kwanakin Ramadana. Ya hallata ga wanda ya yi niyya tun da magriba a kan ya ci, ya sha, ya yi jima’i da matarsa har zuwa alfijir. Wanda bai yi niyya ba tun daren farko na ganin wata to ba shi da azumi.

Tsarki Daga Jinin Haila Ko Jinin Biki: Mace mai haila ko jinin biki ba za ta yi azumi ba, kuma ba za ta yi salla ba. Amma za ta rama dukkan azumin da ta sha, ban da sallah. Ba za ta rama sallah ba. Ya wajaba ga mace mai haila ko jinin biki ta duba farjinta da ‘yar auduga, ko farin kyalle a kusan fitowar alfijir, don ta gani ko azumin gobe zai wajaba a kanta, za ta yi haka ne saboda ta gane ko jinin ya tsaya.

Hankali: Babu azumi akan mahaukaci, kuma bai inganta ba, amma zai rama dukkan azumin da ya sha bayan warkewarsa.

Balaga: Azumi bai wajaba a kan yaro ko yarinya wadanda ba su balaga ba.

Musulunci; Babu azumi a kan kafiri.

Samun Iko: Azumi bai wajaba ba a kan wanda ba ya iya yinsa domin ciwon kishirwa ko ciwon yunwa ko don tsufa tukuf.

Barin Yin Jima’i Ko Fitar Da Maniyyi, Ko Maziyyi Da Rana, Da Barin Shigar Da Wani Abu A Cikin Ciki Da Rana:  Wanda ya yi daya daga cikin wadannan babu azuminsa. Mutum ko da tsakuwa ce ya hadiye har ta kai ciki, azuminsa ya karye. Idan kuwa abu ruwa-ruwa ne, da ya kai ga makogoro, shikenan azumi ya karye don ba ya yiwuwa ya maido shi baya. Kofofin jiki wadanda idan wani abu ya shiga ta cikinsu har ya kai ciki azumi zai karye shida ne kawai. Su ne: Baki, hanci, idanu, kunnuwa, dubura da farjin mace. Dura magani ko wani abu ta kofar zakari ko ta wani kurji mai zurfi daura da ciki ba zai karya azumi ba kamar misali (yin Allura).

Haka kuma idan mace ta shafa tozali tun gabanin alfijir ko kuma mutum ya saka magani a cikin hancinsa, to, ko maganin ya gangaro ga makogoro da rana, azumi bai karye ba. Abin da dai aka hana shi ne aikata dayan wadannan bayan fitowar alfijir, wannan kam azumi zai karye idan sun gangaro ga makogwaro.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma
Manyan Labarai

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah
Manyan Labarai

Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah

November 7, 2025
Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump
Manyan Labarai

Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump

November 7, 2025
Next Post
Manoman Rani Na Sa Ran Samar Da Shinkafa Da Alkama Mai Yawa A Taraba

Manoman Rani Na Sa Ran Samar Da Shinkafa Da Alkama Mai Yawa A Taraba

LABARAI MASU NASABA

Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma

November 7, 2025
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 3.6 Cikin Dari A Watanni 10 Na Farkon Shekarar 2025

November 7, 2025
An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

Kasar Sin Za Ta Dage Dakatar Da Shigo Da Waken Soya A Kan Kamfanonin Amurka Uku 

November 7, 2025
Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

Abin Da APC Za Ta Yi Da Rinjayen Kashi Biyu Bisa Uku A Majalisar Tarayya

November 7, 2025
An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

An Yi Kira Da A Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Afirka Don Bunkasa Masana’antu A Sassan Afirka

November 7, 2025
APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP

Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna

November 7, 2025
Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi

November 7, 2025
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Halarci Taron COP30 A Brazil

November 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.