• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Maraba Da Watan Ramadan

byShehu Ismaila Umar Mai Diwani
7 months ago
Ramadan

A’uzu billahi minash shaidanir rajim, bismillahir rahmanir Rahim. Allahumma Salli ala Sayyidina Muhammadin Alfatihi lima uglika wal khatimi lima sabaka nasiril hakki bil hakki, wal hadi ila siradikal mustakim wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim. Wa radiyallahu an as’habi Rasulullahi (SAW), wa la haula wala kuwwata illa billahil aliyyil azim. Ya himmatas Sheikh, ihdirilana bi hazal mahdari wal ta’adifi binazaratin ta’ati lana bizzafari.

Alhamdu lillah. Mun gode Allah da ya nuna mana karatowan wannan sabon wata na Ramadana, wata mai alkhairi, mai albarka, wata mai dukkan wani abu na falala da za a fada, muna fata wurin Allah ya azurta mu da azumtarsa, Allah ya buda wa al’ummar musulmi da abin da za a ci, a sha, Allah ya dauke mana dukkannin musifu albarkacin wannan watan.

  • Hakuri Da Baiwa (Kyautar) Manzon Allah (SAW)
  • Wasu Ruwayoyi Game Da Yafiyar Manzon Allah (SAW)

Hukuncin ganin watan Ramadan

Muslim ya fitar da Hadisi daga Abdullahi bin Umar ya ce manzon Allah (SAW) ya yi magana a kan azumi, cewa “Inna ummatan ummiyyatan – mu al’umma ce ba’umma” sai da ya yi ishara da hannunsa, yana nuni da yatsun hannayensa guda goma, ya yi nuni da su sau biyu, na ukun sai ya kulle babban yatsarsa, yana nufin tara (goma sau biyu, sai tara), Annabi (SAW) yana nufin in kuka yi azumi 29 aka ga wata ku sha ruwa, (Sumu li ru’uyatihi, wa afdiru li ru’uyatihi, wa’in gumma alaikum fakdiru salasina – ku yi azumi in an ga wata, ku sha ruwa in an ga wata, idan ba a ga wata a 29 ba, ku kudurce yin Talatin).

Wurin maganar ganin wata, kowacce kasa ana yi mata hukunci ne da Sarkin Musulmi, duk masarautun da ke karkashinsa sai su ba shi rahoton ganin watan, in wancan garin ba su gani ba wani garin za su gani, in Sarki ya yarda, azumi ya zama farilla a kan duk musulmin garin amma in duk garuruwan ba a gani ba sai a shirya cika talatin.

LABARAI MASU NASABA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

Har ila yau yana daga hukuncin shari’a, ba a fara azumi da kokwanto, misali ka kwanta bacci sai ka kudirce a ranka cewa in an bayyana ganin wata ina bacci, zan tashi da azumi. Mun gode Allah, yanzu sabida na’u’rar zamani da wuri ake sanar da ganin wata.

Lamarin ganin watan Ramadana abu ne mai sauki, sabida galibin Malamai da Shehunnanmu na kasa da waje baki daya suna kan Hadisin Kuraibu da yake cewa “Kowacce kasa da ganin watanta, misalin kasar: Nijer da Ghana, Mali, Togo da dai sauransu duk suna da Sarkin Musulmi kuma shi zai ayyana ganin watan.

Amma kuma, in Nijer suka ga watan Ramadana, Sarkin Musulmin Nijeriya in yaga dama zai iya cewa na ga wata da ganin watan Nijer sabida dare da lokutan kasashen duk iri daya ne. Sai dai ban da kasar da lokutansu ba iri daya ba ne – ra’ayin wasu malamai kenan.

Amma a wannan zamani na kimiyya da fasaha, Allah shi ne zamani. Annabi ya ce ba ma Hisabi, ba ma Rubutu (ba wai ya hana ba ne) Littafinsa ne ma ya yi nuni da a yi Karatu “Ikra’a” Allah kuma ya yabi masu Rubutu “Bi’aidi safarah, kiramin bararah” sabida muhimmancin karatu da rubutu, a ranar yakin Badar, Annabi (SAW) ya yanke wa duk fursunoni fansa amma ya ce duk wadanda suka iya karatu da rubutu su karantar da yaran Madina, wannan shi ne fansarsu.

Allah ya kawo Kimiyya da fasaha da za a iya ganin abin da ido ba zai iya gani ba daga nesa (Telescope) sabida haka duk duniyar Malaman Musulunci suka yi fatawa cewa yanzun in Makkah ta ga watan Ramadana to duk Musulmi su dauki niyyar azumin.

In Sarkin Musulmi ya ga dama ya yi amfani da hadisin kuraibu, tafiyar iyaye da kakanni cewa kowacce kasa da ganin watanta, Sarkin Musulmi ya yi dai-dai, in ya amshi sabuwar fatawa, sabida Hadisin “Sumu li ru’u’yatihi, wa afdiru li ru’u’yatihi – ku yi azumi in kun ga wata sannan ku ajiye in kun ga wata.” Hadisin ya nuna cewa Annabi (SAW) ya hade Jama’arsa duka gaba daya.

In an ce Makkah, kar ka kalli wadanda suke cikin garin, ka yi amfani da garin, shi ne wanda Annabi ya zauna a ciki, tushen Addinin Musulunci.

Dangane da garuruwan da ba su da dare kuwa, kullum rana ce, su kaddara wata, su yi amfani da lokaci, a tsakiyar rana amma lokacin sahur ne ko kuma a tsakiyar rana amma lokacin shan ruwa ne.

In wani musulmi ya ga wata amma Sarkin Musulmi bai amsa maganarshi ba, to shi wanda ya ga watan azumin ya hau kanshi, sai ya azumci azumin a boye sabida girmama hukuma. Addini ya hana Jama’a ta zauna ba shugabanci.

Hadisin kuraibu, tulin Malamai da Shehunnai suna kan wannan Hadisin kuma wayayyu ne sun yarda da zamani.

Hadisin Kuraibu, Muslim ne ya ruwaito shi kuma ingataccen Hadisi ne, Ummul Fadli binti Haris, Matar Abbas dan Abdulmudallib ce ta aiki Kuraibu Sham, wajen Mu’awiya. Kuraibu yake cewa, bayan na isar da sakonta ina Sham, sai azumi ya riske ni ina can, mun ga jinjirin watan Ramadana ranar Alhamis da dare, bayan na dawo Madina, sai Abdullahi dan Abbas ya yi mun zance kan watan, ya tambaye ni yaushe muka ga watan Ramadana a Sham, sai na ce masa ranar Alhamis da dare, sai ya ce min kai ma Allah ya azurtaka da ganin shi? Na ce masa eh, Jama’a da dama sun gan shi, har Khalifa Mu’awiya ma ya yi Azumi, Abdullahi dan Abbas ya ce masa amma mu sai daren Asabar muka ganshi, kuma za mu ci gaba da azumi har sai mun yi 29 ko 30, Kuraibu ya ce masa shin ba za ka wadatu da ganin wata da azumin Khalifa ba, Abdullahi ya ce a’a, ba zan wadatu da ganinsu ba, haka Annabi (SAW) ya umurce mu, kowacce al’umma da ganin watansu.

Wannan Hadisi ingatacce, galibin malamai suna kan shi amma malamai na zamani masu ilimi da fahimta sun tafi cewa tun da Allah ya kawo wadannan ci gaba na kimiyya da fasaha, ba laifi in Sarkin Musulmi ya yarda da ganin watan Makkah ya ce al’ummar Musulmi na duniya su tashi da azumi a rana daya.

An karbo daga Hafsatu Ummul Muminina ta ce Manzon Allah (SAW) ya ce “Duk wanda bai yi niyyar Azumi ba kafin Asubah, bai da azumi”

Ba laifi, mutum zai iya kudurce niyyar yin azumin Ramadana 29 ko 30 a daren azumin farko bayan an sanar da ganin watan ko kuma ya kudurce niyyar azumin ko wacce rana na daga watan ramadana din. Amma ka kwanta bacci da nufin cewa in an ga watan zan ci gaba da azumi in ba a gani ba shikenan, hakan shari’ah ba ta yarda ba.

Azumin watan Ramadana wajibi ne ga dukkan Musulmi baligi mai lafiya ba mara lafiya ba, wajibcin azumi kamar yadda Allah ya fada a cikin Al’kur’ani da fadarsa yana cewa: “Ya ku Muminai Allah Ya wajabta muku yin azumi kamar yadda ya wajabta ma wadanda suka zo kafin ku, ko za ku ji tsoron Ubangijinku. Kwanaki ne kididdigaggu, wanda ya kasance a cikinku bai da lafiya ko kuma yana kan tafiya, to ya rama abin da ya kubuce masa a wasu ranakun, wadanda kuma ba za su iya yin azumin ba, to su ciyar da Miskinai, amma wanda yake da damar ciyar da miskinai da yawa, to ya yi alkairi ne a wajenshi, lallai yin azumin ya fi alkairi a gare ku, idan kun san wannan alkairin da ke cikin azumin.”

Haka nan a aya ta gaba, Allah ya ce, “Lallai watan Ramadana da aka saukar da Alkur’ani a cikinshi, shiriya ne ga mutane, sannan kuma akwai ayoyi bayyanannu a cikinshi masu shiryarwa zuwa ga Allah da bayyana hukunce-hukunce. Duk wanda ya halarci ganin watan to ya azumce shi, wanda kuma bai da lafiya ko kuma yana kan tafiya, to ya biya abin da ya tsere masa a cikin sauran wasu ranakun, Allah sauki yake nema daga wurinku ba wahalarwa ba, Allah yana son ku cika adadin azumin, sannan yana son ku yi masa kirari daga abin da ya shiryar da ku, ko za ku gode masa?”.

 

Saukar Da Alkur’ani Da Littafan Manzanni

Allah ya saukar da mafificin Littafi (Alkur’ani) a cikin watan Ramadana, a mafificin dare (Lailatul Kadri).

An karba daga Abdullahi bin Abbas, Allah ya yarda da su, yake cewa “Allah Ya saukar da Alkur’ani daga Lauhil Mahfuzi izuwa saman Duniya (a cikin Ramadana aka saukar da Alkur’ani daga Lauhil Mahfuzi zuwa saman Duniya, a dakin Baitul ilimi), Mala’ika Jibril (AS) shi kuma daga nan yake debo ayoyinsa zuwa ga Annabi (SAW), sai da ya shafe shekaru 23 yana kan wannan aikin.

An karba daga Wa’ilatu bin Asda’in ya karba daga manzon Allah (SAW) cewa an saukar da littattafan Annabi Ibrahim (AS) a daren farko na watan Ramadana; Littafin Attaurar Annabi Musa (AS), ta sauka a daren bakwai na watan Ramadana; Injilar Annabi Isa (AS) ta sauka 13 ga watan Ramadana; sai Alkur’anin Annabi Muhammad (SAW) ya sauka daren 14 ga watan Ramadana.

Abdullahi bin Abbas ya ce, Annabi SAW ya fada wa wata Mata daga cikin Mutanen Madina cewa idan Ramadana ya zo, ta je ta yi Umra, domin yin Umra a cikin watan Ramadana daidai yake da aikin Hajji, Nasa’i ya ruwaito Hadisin.

Allah ya ba mu damar azumtar wannan azumin gabaki daya, Allah ya buda wa ‘yan uwa musulmin duniya da abin da za su ci su sha, Allah ya bai wa kasarmu Nijeriya zaman lafiya. Allah ya saka wa iyayenmu na Zawiyya da alkairi wanda da albarkarsu da karfin Allah muke gudanar da wannan lamarin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi
Dausayin Musulunci

Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi

October 3, 2025
Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)
Dausayin Musulunci

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (3)

September 26, 2025
Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

September 5, 2025
Next Post
GORON JUMA’A

GORON JUMA'A

LABARAI MASU NASABA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version