ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, June 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wasu Ruwayoyi Game Da Yafiyar Manzon Allah (SAW)

by Sulaiman
1 year ago
Manzon Allah

An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai hukunta wani matsafi (Labidu) da ya yi masa tsibbo ba. Labido shi ne matsafin da ya yi wa Annabi (SAW) tsafi, wata rana ya ji jikinshi babu dadi kamar an kukkule shi, bayan ya kwanta bacci, sai ya yi mafarki da Mala’iku biyu, daya ya tsaya a wurin kai dayan kuma ya tsaya a wurin kafafunsa, sai daya ya tambayi daya, wai me ke faruwa da wannan Mutumin? Sai ya ba da amsar cewa, Asiri aka yi masa, waye ya yi masa? Labidu dan La’asa, a ina ya boye sihirin? A cikin rijiyar banu Zarwana, Meye maganin Sihirin? Ya karanta Suratu Falaki da Nasi. Take Manzon Allah (SAW) ya farka, ya aiki Sayyadina Aliyu da Zubairu bin Awwam, ya ce su shiga cikin rijiyar su dauko sihirin, Sayyadina Ali ne ya shiga cikin rijiyar ya dauko sihirin, an ruwaito cewa, sabida tsabar dafin sihirin duk Ruwan rijiyar ya zama kalan ja, kamar Ruwan lallen da mata ke kwalliya da shi. Sai ya daura wani katon dutse akan sihirin. Bokan ya zana mutum-mutumin Annabi (SAW), ya tsitstsira allura goma sha daya (11) sannan ya hada da gashin Annabi (SAW) ya daure a duk gabobin mutum-mutumin da ya zana na Annabi (SAW). Bayan dawowarsu wurin Annabi (SAW) sai ya karanta Falaki da Nasi, kowacce Aya in yakaranta sai gashin ya warware, Annabi (SAW) ya ce sai na ji kamar an kwance ni a cikin Mari. Shi ma Annabi (SAW) ya yafe masa.

Haka nan kuma, Annabi (SAW) bai kama Abdullahi bin Ubayyu ba (Shugaban Munafukai) da sauran munafukai duk da mugayen maganganun da suke gaya masa “la’in raja’ana ilal Madinati, layukrijannal a’azzu minhal azal… in mun dawo gida Madina, sai masu girma sun kori kaskantattun daga cikin Madina”. Allah ya ba su amsa da cewa “wa lillahil izzatu wa lirasulihi wa lil muminina wa lakinnal munafikin la ya’alamun”, girma na Allah ne da Annabinsa da Muminai sai dai su Munafukai ba su sani ba”. Manzon Allah (SAW) ya gaya wa wasu daga Sahabbansa da suka ce Annabi (SAW) ya kashe Munafukai cewa, in ya kashe su za a koma ana cewa ya fara kashe Mutanensa, babu wanda zai lura da laifin da suka yi.

  • Hankali Da Ilimin Annabi Muhammadu (SAW)
  • Kyawawan Dabi’un Annabi Muhammadu (SAW)

An karbo Hadisi daga Anas bin Malik (Khadimin Annabi (SAW) fiye da Shekara 10) yana cewa, sabida Albarkar hidimar da ya yi wa Annabi (SAW), sai da ya binne ‘ya’ya 100 ban da wadanda suka rayu, sannan kuma Allah ya ba shi dimbin dukiya ga zinarai ba adadi da gonakai da gidaje.

ADVERTISEMENT

Anas yana cewa, wata rana Ina tare da Annabi (SAW) yana yafe da mayafi mai kwarin gefe (cin baki) sai wani Balaraben kauye ya zo ya fuzgo mayafin daga jikin Annabi (SAW) har sai dai shaidar fizga ta fito a wuyan dokin Annabi (SAW) sannan kuma Balaraben kauyen ya ce, Ya Muhammadu ka daura min dukiyoyin Allah (Zakkah) da ake ba ka a kan Rakumana guda biyun nan sannan kuma ba burge ni ka yi ba sabida ba kudinka ba ne, na Allah ne ake tarowa, sai Annabi (SAW) ya yi shiru sannan ya ce “wallahi dukiya ta Allah ce, haramun ne ni na ci, amma ni bawansa ne, ni dan rabo ne, dukiya ta Allah ce kuma zan ba ka, ni kuma kana so a saka min a kan abin da ka yi min?” sai ya ce, A’a, sai Annabi (SAW) ya ce masa sabida me? Sabida ba ka rama mummuna da mummuna, sai (SAW) ya yi murmushi ya ba da umurnin cewa, a daura wa Rakumi daya buhunan Alkama iya karfin rakumin sannan a daura wa dayan buhunan Dabino iya karfin rakumin.

Sayyada A’isha tana cewa, ban taba ganin Annabi (SAW) yana fadar kare wa kansa ba kan wata cuta da wani ya yi masa sai dai in an keta alfarmar Allah. Duk soyayyar da Annabi (SAW) ke yi wa Mu’azu bin Jabal amma da ya zagi Bilal a gabansa, sai da Annabi (SAW) ya ce masa “Mu’azu har yanzun akwai halin Jahiliyya a tare da kai”. Khalid bin Walid ya nemi taba wani daga cikin Sahabbai, sai Annabi (SAW) ya ce masa “kar wani don ya musulunta jiya ya ce zai taba min wani daga cikin Sahabbaina,” duk wannan don taba alfarmar Allah ne Annabi (SAW) ke shiga ciki ya rama.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne.

An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje.

An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba.

Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya fizgo rigar Annabi (SAW) daga kafadarsa, ya shake kwalar Annabi (SAW) sai ya ce “Ku ‘ya’yan Abdulmudallib taurin bashi ne gare ku,” sai Sayyadina Umar ya tamka masa da magana mai kaushi, shi kuma Annabi (SAW) yana ta Murmushi, Annabi (SAW) ya ce ya Umar “Da ni da mai amsar bashi, mun fi bukatar wani abu ba irin wannan yadda ka yi ba,” cewa za ka yi “Ya Muhammad, ka dinga kyakkyawan biyan bashi, shi kuma ka ce masa, ba a haka ya dace a dinga zuwa karbar biyan bashi ba,” sauran kwana uku lokacin biyan bashin ya yi. Sai Annabi (SAW) ya umarci Sayyadina Umar da ya biya masa bashin sannan kuma ya kara masa loka Ashirin na hatsin sabida tsorata shi da ya yi, sai wannan ya zama sanadin Musuluntar Bayahuden.

Yadda labarin yake shi ne, wannan Bayahude yana daga cikin manyan malaman Yahudawa, ya kasance yana cewa, tun da ya ga fuskar Annabi (SAW) ya ga alamun Annabtarsa duka sai guda biyu ne kadai bai jarraba ba, su ne: Hakurinsa yana riga fushinsa, tsananin wautar masu wauta ba ta fusata shi sai dai ta kara masa hakuri.

Sabida in tabbatar da wannan ya sa na je don in gwada shi, sai kuma na tabbatar da hakan kamar yadda Attaura ta fada. In ji Malamin Yahudawan (dan Sa’anata)

Hadisai da suke magana kan hakuri da afuwar Annabi (SAW) lokacin da yake da cikakken iko kan komai wurin zartar da hukunci, ya fi karfin a ce za a zo da su baki daya. Amma ya isa ma’auni a ce cikin Kabilar Kuraishawa ya taso kuma ya fara kira da a bi Ubangiji a cikinsu, wautar Jahiliyya a fili take a cikinsu har Allah ya taimake shi ya dora shi a kansu kuma ya hukunta shi a kansu.

Manzon Allah
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya
  • Sulaiman
    Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari
  • Sulaiman
    Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana
  • Sulaiman
    Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

MASU ALAKA

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
Dausayin Musulunci

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

June 12, 2026
Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

June 5, 2026
Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

May 29, 2026
Next Post
Rikicin Uba Sani Da El-Rufa’i Ya Dauki Sabon Salo

Rikicin Uba Sani Da El-Rufa’i Ya Dauki Sabon Salo

LABARAI MASU NASABA

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)

Cututtukan Da Aka Fi Fama Da Su Lokacin Damina Da Yadda Za A Kauce Musu (1)

June 13, 2026
Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

Talauci Ya Sake Karuwa Da Kashi 63 Duk Da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Da Gwamnati Ta Yi – IMF

June 13, 2026
Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

Muhallin Halittu Da Aka Yi Gado A Kasar Sin Sun Samu Ci Gaba Ta Fuskar Ba Su Kariya

June 13, 2026
Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

Gwamnonin Arewa-maso-yamma Sun Kaddamar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Yankin

June 13, 2026

Sake Jan Damarar Soja Da Japan Ke Yi Karin Alama Ce Mai Hadari

June 13, 2026
NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

NANS Ta Kafa Kwamitin Ganin Yadda Ake Tafiyar Da Ayyukan TETFund

June 13, 2026
Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

Shugaban Majalisar Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa Ta Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Raya Dangantakar Gabobi Biyu Na Mashigin Tekun Taiwan Cikin Lumana

June 13, 2026
Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

Ghana Za Ta Kai Ƙarar Canada Kotu Kan Hana Thomas Partey Shiga Ƙasar

June 13, 2026
Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

Sin Ta Zama Abin Koyi Na Sauyi Da Ci Gaba Ga Kasashe Da Dama, In Ji Shalva Papuashvili

June 13, 2026
Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

Garkuwa Da Mutane Na Barazana Ga Dalibai Miliyan 1.9 Masu Jarrabawar WAEC A Sassan Nijeriya

June 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.