Matashin dan siyasar nan Mista Mulki Markus Masoyi wani fitaccen dan siyasa a karamar hukumar Bogoro da ke jihar Bauchi ya samu kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane bayan shafe tsawon kwanaki sha hudu a hannunsu.
Shi dai Markus ya samu komawa cikin iyakansa da abokansa ne a ranar Lahadi bayan samun tsira.
- Ba Zamu Daga Kafa Kan Malaman Addini Da Ke Kokarin Haddasa Rikici A Nijeriya Ba – DSS
- Kwalejin Confucius Ta Yi Bikin Cika Shekaru 10 Da Fara Aiki A Saliyo
Lokacin da ya dawo gida, ya wallafa hotunsa inda ke gode wa Allah bisa samun kubutar da ya yi, ya kara da cewa, tsirar da ya samu bai samu ba sai da addu’o’in jama’an ‘yankinsu.
“Ina son na yi amfani da wannan damar na gode wa Allah da kuma dukkanin wadanda suka yi ta mun addu’ar neman tsira, kalmomin baki ba za su iya bayyana irin farin cikin da nake ji ba”.
Idan za ku iya tunawa dai masu garkuwan da farko sun tuntubi iyalan Masoyi inda suka ce sai an basu naira miliyan 100 kafin su sake shi.
Da yake tofa albarcin bakinsa kan wannan matakin, Shugaban kungiyar bunkasa yankin Boi, Rabaran Philemon Kicheme, ya ce, masu garkuwan sun saki matashin dan siyasan ba tare da illata shi ba, sai dai bai yi bayani kan an biya kudin fansar ko akasin haka ba.
Daga bisani ya gode wa jami’an tsaro da ‘yan jarida da al’ummar yankin a bisa rawar da suka taka wajen ganin an sako dan siyasan.