Kungiyar kwallon kafa ta Marseille da ke ƙasar Faransa ta karrama tsohon dan wasan Nijeriya, Tayo Taiwo, ta hanyar saka sunansa a cikin jerin sunayen tsofaffin ‘yan wasan da suka bai wa kungiyar gudunmawar da ba za a manta da su ba.
Tsohon dan wasan bayan, wanda ya bugawa kungiyar wasa daga shekara ta 2005 zuwa 2011 ya kasance jigo a lokacin da yake bugawa kungiyar wasa kuma ya shafe shekaru shida yana wakiltar Marseille din.
Taye Taiwo dai ya zura kwallaye 25, sannan ya taimaka an zura guda 23 cikin wasanni 271 da ya bugawa kungiyar ta ƙasar Faransa. Sannan ya wakilci Nigeria sau 54 daga shekara ta 2004 zuwa 2011 inda ya zura kwallaye biyar.
Tsohon dan wasan ya bugawa manyan kungiyoyi a nahiyar Turai wasa kamar AC Milan da Queens Park Rangers ta Ingila.
A shekara ta 2019 ya yi ritaya daga buga wasan kwallon kafa yana da shekara 39 a duniya kuma kawo yanzu yana zaune a ƙasar Faransa.
Saka sunan Taye Taiwo a cikin jerin zakakuran yan wasan kungiyar ya nuna yadda dan wasan ya nuna bajinta da kuma yadda ita kanta kungiyar ta Marseille ta yaba da irin kokarin da ya yi a baya.