Mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya yi ikirarin cewa shi ma dan kabilar Igbo ne.
Okowa, wanda ya fito daga yankin Igbo na karamar hukumar Ika ta Arewa da ke yankin Delta a yankin Kudu maso Kudu, ya ce ya cancanci a kira shi dan kabilar Igbo sabida kabilar Igbo, sun karade duk fadin kasar Nijeriya.
Jaridar Pulse ta ruwaito cewa a kwanakin baya ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya tsayar da Okowa a matsayin abokin takararsa a zaben 2023 mai zuwa.
Gwamnan jihar Delta, Okowa ya doke takwarorins na Rivers, Nyesom Wike da Udom Emmanuel Na Akwa Ibom, inda ya zama mataimakin dan takarar shugaban kasa a PDP.
Sai dai Okowa ya fuskanci suka musamman daga masu ruwa da tsaki da kuma dattawan yankin Kudu maso Gabas, inda suka yi masa lakabi da wanda ya ci amanar kabilar Igbo da ya tare damar dan kabilar Igbo ya zama mataimakin shugaban kasa.