Babban mai neman kujerar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, bai halarci taron bikin kaddamar da takwaransa na jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba a ranar Alhamis.
Idan zaku tuna cewa Wike ne ya zo na biyu a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a ranar 28 ga watan Mayu da kuri’u 237, inda Atiku Abubakar ya samu kuri’u 371.
- 2023: Atiku Ya Gabatar Da Gwamnan Delta, Okowa A Matsayin Mataimakinsa
- 2023: Atiku Ya Gana Da Gwamnonin PDP Kan Zabo Masa Mataimaki
Tun bayan zaben fidda gwanin da aka yi, Wike ya kasance dan takarar shugaban kasa na zahiri ga Atiku ganin irin tasirin da gwamnan ke da shi a cikin jam’iyyar.
Sai dai kuma tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar da Okowa a gaban jiga-jigan jam’iyyar da manyan jami’ai a hedikwatar PDP ta kasa da ke Abuja.
Ya ce daya daga cikin abin da yasa ya zabi Okowa shi ne cancantarsa saboda kuma ya gaje shi bayan ya yi mulki idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.
“Na yi farin cikin sanar da Gwamna Ifeanyi A. Okowa a matsayin dan takararar mataimakin shugaban kasa. Ina fatan tafiya tare da ahi wajen gina kasarmu mai girma tare da daukacin ‘yan Nijeriya da samar da alkibla guda ta zaman lafiya, hadin kai, da wadata ga kowa,” in ji Atiku.
Bayan shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC), kwamitin amintattu (BoT), da ‘yan jam’iyyar Caucus, abokan aikin Okowa ma sun halarci bikin kaddamar da bikin.
Sun hada da gwamnonin jihar Enugu, Ifeanyi Uguanyi: Bauchi, Bala Mohammed; Awka Ibom, Udom Emmanuel; Edo, Godwin Obaseki, da Benue; Samuel Ortom.