Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce duk da yake tattalin arzikin Nijeriya na fuskantar ƙalubale, kwatanta shi kafaɗa-da-kafaɗa da na Venezuela da gwamnonin jam’iyyar PDP su ka yi rashin adalci ne.
Ya ce: “Mu na bayyana cewa, duk da yake ƙasarmu na fuskantar wasu matsaloli, waɗanda kuma wannan gwamnati ta Shugaba Tinubu na ƙoƙarin magancesu, amma matsalolinmu ko kusa ba su kai irin na kasar Venezuela ba, kamar yadda gwamnonin PDP su ka yi zargi.”
- Adadin Zirga-zirgar Fasinjoji A Jiragen Kasa Ya Zarce Miliyan 230 A Rabin Farko Na Wa’adin Hutun Bikin Bazara
- Nijeriya Za Ta Shawo Kan Ƙalubalen Da Take Fuskanta Nan Gaba Kaɗan – Ganduje
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ministan ya ce: “Tattalin arzikin Nijeriya har yanzu ya na da ƙarfi sosai, kuma ana sa rai da kyakkyawan hasashen cewa zai bunƙasa da ƙarin kashi 3 cikin 100 cikin wannan shekarar.
“Tattalin arzikin mu na bayar da gudunmawar lamuni ga masu rance a cikin gida da waje.”
A ranar Litinin ne Gwamnonin PDP su ka gudanar da taro a Abuja, inda suka tattauna batutuwa, musamman waɗanda su ka shafi matsalar tsaro da matsalar tattalin arziki, wacce ta haifar da tsadar rayuwa.
Bayan kammala taron, sun bada sanarwar cewa, sun amince kowace jiha a ba ta damar kafa ‘yansandan jiharta, domin shawo kan ƙalubalen matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.
Amma a martaninsa, Ministan ya ce, “Mu na maraba da shawarwarin da su ka bayar waɗanda ba na son rai ba, domin ganin an magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki.
“A matsayinsu na shugabanni a gwamnatocin jihohi, gwammonin PDP su na da ‘yancin bayyana matsayarsu kan duk wani abu da ya shafi ƙasar nan.
“A matsayin gwamnonin PDP, waɗanda ya kamata a ce masu shiga sahun gaba ne kan inganta tattalin arziki, samar da yalwa a ƙasa da al’ummar jihohinsu, a ce kuma sun koma su na furta kalaman ƙage da shaci-faɗi kan Nijeriya, har su na kwatanta matsalar tattalin arzikin Nijeriya da irin matsalolin da su ka dabaibaye tattalin arzikin Venezuela.
“Mu na son mu bayyana cewa duk da yake dai tattalin arzikinmu na fuskantar ƙalubale, amma ko kusa ba daidai ba ne a kwatanta matsalar Venezuela da ta Nijeriya.
“Yayin da Gwamnatin tarayya ke biyan albashi da sauran haƙƙoƙin ma’aikata kan kari, kuma harkokin gwamnati na tafiya daidai-wa-daida, ya kamata ‘yan Nijeriya su tambayi gwamnonin PDP abin da su ka yi da kuɗaɗen da ake ba su.
“Saboda akwai rahoton bincike mai nuna cewa, yawancin jihohin PDP sun kasa biyan ‘yan fansho kuɗaɗensu na tsawon watanni da dama, haka albashin ma’aikata ma wasu ba su biya yadda ya kamata.
“Gwamnonin PDP na ƙin biyan garatutin ma’aikatan da su ka yi ritaya.
“Haka kuma wasu gwamnonin PDP ɗin har yau sun kasa biyan naira 30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, shekaru huɗu da Gwamnatin Tarayya ta fara amfani da tsarin.”