Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta tabbatar da cewa dan wasanta na baya, Lisandro Martinez, zai yi jinya ta watanni biyu, bayan ya gurde a kokon gwiwarsa ta dama.
Bayan tashi daga wasan kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya ce raunin da Lisandro Martinez ya ji mai muni ne bai da kyawun gani, sai dai daga baya an gano cewa raunin ba shi da muni sosai.
- AFCON 2023: Za A Kece Raini Tsakanin Nijeriya Da Cote de’Voire A Wasan Karshe Ranar Lahadi
- Ina Da Labarin Sirri ‘Yan Bindiga Za su Kawo Mun Farmaki – Gwamna Dikko Raɗɗa
Mai tsaron bayan ya rike kafarsa yana sharbar kuka lokacin da ya ji ciwon a wasan Premier League da United ta ci West Ham 3-0 ranar Lahadi, kuma wasa na uku da Martinez ya buga kenan a Premier League, bayan da ya dade yana jinya.
Ten Hag ya ce ya damu da raunin da mai tsaron bayan ya ji, kuma zai zamar masa koma baya a kakar nan kuma Martinez ya ji rauni a zagaye na biyu, bayan da ya yi kokarin tare kwallo daga wajen mai tsaron bayan West Ham, Bladimir Coufal.
Dan Kasar Argentina ya buga wasa na uku a United, bayan sama da wata uku da ya yi jinyar rauni a kafa, sannan wasa 22 ne Martinez bai buga ba, sakamakon jinya, wanda ya samu komawa buga wasa a karawar da United ta yi da Tottenham ranar 14 ga watan Janairu.
Ranar Lahadi United ta doke West Ham 3-0 a wasan mako na 23, hakan ya sa ta koma mataki na shida a kan teburi da maki 38 sannan United za ta kara a wasan mako na 24 a Premier League ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu, inda za ta ziyarci Aston Billa a Billa Park.
Sannan a kuma ranar ce West Ham za ta karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a wasan hamayya tsakanin kungiyoyin Landan a babbar gasar firimiya ta Ingila.