Matashin marubucin dan asalin Jihar Kano, wanda ya yi fice a fagen rubutun labaran yake-yake, kuma mai rike da sarautar ‘Sarkin Samarin Marubuta Adamu Tukur Miyetti ya yi wannan ikirari ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu Adamu Yusuf Indabo. Ko me ya sa marubucin ya furta haka? To ga dai cikakkiyar hirar don jin yadda ta kaya.
A matsayinka na marubuci, kuma memba a kungiyar Hausawan Afirka. Wanne tanadi marubuta suke yi wa Ranar Hausa Ta Duniya, kuma wanne tanadi kungiyarku take wa wannan rana?
- An Kori Shugaban Jam’iyyar APC Na Jihar Zamfara Tukur Danfulani Daga Jamiyyar
- Kungiyar Fulani Ta MACBAN Ta Nesanta Kanta Daga Zanga-zangar Matasa
Marubuta sun yi wa ‘Ranar Hausa Ta Duniya’ ta wannan shekarar ta 2024 tanadin yin rubuce-rubuce domin tabbatar da harshen Hausa ya zama harshen da za a yi amfani da shi a makarantu da mu’amaloli na kasashen Afirka guda 54 baki daya, domin saukaka wa yaranmu iya fahimtar karatu. Kasancewar ingilishi da faransanci kayan aro ne da aka ce ba ya rufe katara. Don haka marubuta suka kudurci yin rubuce-rubuce na yin kira da wayar da kai a kan muhimmancin sanya harshen Hausa don ya zama yaren kasa a dukka kasashen Afirka baki daya. Kuma muna sa ran hakarmu za ta cimma ruwa.
Mene ne alfanu da tasirin ranar Hausa ga al’umar kasar Hausa?
Ranar Hausa ta duniya tana da alfanu da kuma tasiri, domin rana ce da majalisar dinkin duniya ta ware domin tunawa da Hausa da Hausawa, kuma su yi bukukuwan al’adunsu, su kuma san muhimmancin al’adun nasu. Idan ranar ta zo, Bahaushen Mutum ko tunawa ya yi da asalin kabilarsa, ya kuma ga al’adunsa na da, da watakila wasu ma bai San su ba, sun yi masa tasiri kwarai da gaske. Kuma za su taimaka masa ya san harshensa na da muhimmanci da al’adu na alfahari da dogaro da su, ba wai yana yin kwaikwayon al’adun wasu ba.
Wacce shekara ce aka ware ko tabbatar da wannan rana ta 26, August a matsayin ranar Hausa ta duniya?
An Samar da ‘Ranar Hausa Ta Duniya’ ne a shekarar 2018 wanda ‘BBC Hausa’ suka samar bisa taimakon Abdulkadir Aliyu. Da ana yin shirin ranar Hausa Ta duniya a kafafan sadarwa na yanar gizo, sai aka ga kyautuwar a dinga yinsa a garuruwa da kasashe mabambanta.
Shin kowacce irin gudummawa harshen Hausa yake ba wa al’ummar duniya da har ya samu wannan tagomashin?
Harshen Hausa ya ba wa al’ummar duniya dugummawa mai tarin yawa sosai da sosai, ta hanyar cinikayya da cudanya da kuma zama lafiya, da kyakkyawan mu’amalla. Wannan suna daga cikin dalilan da ya sa Bahaushe yake da kima da mutunci a idon duniya baki daya.
Tunda muna magana ne a kan Hausa, to shin wai wanene Bahaushe?
To a har kullum ina fada cewa Bahaushe shi ne wanda dabi’unsa da halayyarsa da abubuwan da yake yi na yau da kullum, kaso saba’in cikin dari yana yi ne da Hausa. Haka masana sukan siffanta asalin Bahaushe da cewa: gajere ne tittirna mai jajayen idanu, gashin kansa a murmurde, kuma mazansu da matansu ba su da yalwar gashi, Bahaushe mai tumbi ne da katon kai, hancinsa gajere ne ba dogo ba. Sai dai dalilin auratayya da wasu kabilu mabambanta ta sa kamannin Bahaushe na asali suka canja, har ya zama ana iya samun Bahaushe dogo santalele kuma mai dogon karan hanci. Wata kila wannan shi ne dalilin da ya sa wasu daga cikin masana suke cewa, ai Bahaushe a yau shi ne wanda kakanninsa bakwai na wajen uwa Hausawa ne, bakwai na wajen uba ma Hausawa ne. To wannan shi ne Bahaushe kuma shi ma sai in ta siffantu da wadancan siffofi na Bahaushe da aka ambata. Amma ni na ce duk mutumin da zai’unsa, da cimarsa, da suturarsa kaso saba’in na Hausawa ne to wannan shi ne Bahaushe.
To a matsayinka na marubuci, za mu so ji daga bakinka, wai waye marubuci kuma wacce irin gudummawa yake bayarwa ga harshen Hausa da Hausawa?
Marubuci wani malami ne da yake iya isar da sako ba tare da yin amfani da aya ko hadisi ba kuma a karu a fadaku. Sannan marubuci mizani ne na iya rusa duniya ko kuma gyara ta, domin aka ce idan mutun mai ilimi daya ya yi ta’asa, to fa sai a tara masana dubu ba su iya warware wannan ta’asar ba. To duk wanda ya kasance marubuci idan ya yi ta’asa, sai an samu irin wannan mutanen da suke da fikira irin nasa, su kadai ne za su iya warware wannan ta’asar. Kuma marubuta ai Hausawa kawai suke ba wa gudummawa ba, addinai da dama marubuta sun ba su gudummawa, da yaruka, da dabbobi, da duk wata halitta ta duniya marubuci ya ba ta gudummawa. Don haka ba iya Hausawa kawai marubuta suka ba wa gudummawa ba. Bayan haka kowa fa ya zama mai ilimi, ko malami ai ya zama ne da taimakon marubuci, saboda ko me mutum ya je ya karanta to marubuci ya riga shi zuwa gurin. Saboda shi ne ya rubuta abin da Malamin ya zo ya koyar da shi. Don haka marubuci ya fi karfin wasa.
Kungiyarku ta Hausawan Afirka, ko mene ne tasirinta ga harshen Hausa da kuma Hausawan Afirka da aka kafa kungiyar domin su?
Kungiyar ‘Hausawan Afirka’ tana da tasiri duba da gudummawar da take bayar wa wajen hade kawunan Hausawan Afirka gaba daya, sun zama suna magana da murya daya, kuma suna mu’amala da zumunci da juna. Sannan kungiyar ta taka muhimmyar rawa wajen tabbatar da ranar Hausa ta duniya ta wanzu ana yin ta a ko’ina. Ba kungiyar ce ta samar da ranar Hausa ta duniya ba, amma kungiyar tana iyakar kokarinta wajen dada yada shi ga Hausawan Afirka baki daya don su kuma rungumi shi wannan harshen nasu su rike shi hannu biyu da gaskiya.
Shin ko marubuta da sauran kungiyoyin Hausa kan samu gudummawa daga gwamnati don gabatar da shagalin bikin ranar Hausa?
Marubutan Hausa na Nijeriya ba sa samun wata gudummawa daga gwamnati ko wasu hukumomi, domin shirya tarukan ranar Hausa ta duniya. Dalili kuwa ba sa shiga gwamnati ba su ma san ta ba, musamman marubuta mazauna Kano. Don haka dole ne ma gwamnati ta manta da marubuta saboda ba su kai kansu gare ta ba balle ta san da zamansu. Sauran kungiyoyi na Hausawa kuwa suna iya kokarinsu gurin nemawa kansu gudummawa, kuma suna samu a gurin gwamantin da hukumomi saboda sun shiga gwamnati. Kalubalen ke nan ga marubuta da ba sa shiga gwamnati.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa.