Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya (NDLEA), Birgediya Janal Buba Marwa (mai ritaya), ya gode wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da illahirin ma’aikatansa kan nasarar lashe lambar yabon jaridar LEADERSHIP ta garzon shekarar 2022 da ya samu.
Marwa ya ce, in ba don goyon bayan shugaban kasa da jami’an NDLEA ba, wadanda suke shiga kwararo-kwararo domin gudanar da ayyukan hukumar ba, shi din ba zai kai ga irin nasarorin da ya samu cimmawa a hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyin.
Kan lambar yabon, Marwa ya ce, tabbas hakan zai kara masa kumaji da karsashin zage damtse wajen yaki da fataucin miyagun kwayoyi da dangoginsu a fadin kasar nan.
Da ya ke magana gefen wajen babban taron kamfanin rukunin jaridun LEADERSHIP da bikin mika lambar yabo ga gwaraza da ya gudana a ranar Talata, Marwa ya kara da cewa, “Dole mu gode wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa dukkanin goyo bayan da yake ba mu da kuma karfafarsa wajen ganin mun gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata.
“Kuma dole ne mu jinjina tare da yaba wa jami’an hukumarmu, wandada su ne sojan kafa da suke gudanar da ayyukanmu yadda ya kamata. Ina jinjina ga jami’anmu maza da mata, ba don su din ba, da ban zo nan wajen a matsayin gwarzo ba.
“Wannan lambar yabon za ta kara mana himma, za ta taimaka mana wajen cigaba da yakin da muke yi. A yakin da muke yi muna samun nasarori kuma za mu cigaba da samun nasara.”
Babban taron kamfanin rukinin jaridar LEADERSHIP mai wallafa jaridun Leadership, Leadership Hausa, National Economy da sauransu na 2022 mai taken “Sahihin Zabe Da Tattalin Arziki A Fagen Sauyi”, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranta, ya yin da tsohon Firaministan Kenya, Raila Odinga ya kasance babban bako mai gabatar da jawabi.