Masana da masu tsara manufofi daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya daban daban, da kungiyar tarayyar Afirka AU, da kasashen Afirka, sun jaddada bukatar kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannoni daban daban na ci gaba mai dorewa, yayin da suke halartar tattaunawar baya-bayan nan kan shirin ci gaban duniya ko GDI.
Kwamishinan ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire na kungiyar AU, Mohamed Belhocine a cikin jawabinsa ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta bunkasa zuwa “kyakkyawar abokantakar moriyar juna”. Yayin da ya bayyana hadin gwiwar Sin da Afirka a matsayin wani misali mai haske na hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, wajen tinkarar kalubale da damammaki a duniya a fannoni da dama da aka fi ba da fifiko”, yana mai cewa, shirin GDI da Sin ta gabatar na da karfin kara karfafa dangantakar Sin da Afirka wadda ke ci gaba da bunkasa, tare da fadada hadin gwiwar kasashe maso tasowa.
Belhocine ya ci gaba da cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka ta samu kyakkyawar sakamako bisa moriyar juna a cikin wadannan shekaru. Kana, taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC ya shaida mana fa’idar hadin gwiwar dake tattare da kimiyya da fasaha, da zaman lafiya da tsaro, da magance sauyin yanayi, da ilimi, da aikin gona, da labarai da fasahar sadarwa, da dai sauransu.” (Yahaya)