Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ta ce masu bincike sun tabbatar da wata sabuwar halitta da aka samu a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, wanda aka yi wa lakabi da Niallia Tiangongensis
A watan Mayun 2023 ne, tawagar ‘yan sama jannati ta kumbon Shenzhou-15 ta gano wani samfurin halitta a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin yayin da take cikin da’irarta. An kuma adana ta cikin yanayi mai sanyi, sannan daga bisani aka kawo ta duniyar dan Adam domin gudanar da nazari. Kuma bayan binciken kimiyya da ya shafi nazarin sauyawar yanayinta da tsarin kwayar halittarta da sauransu, masana sun tabbatar da cewa sabuwar halitta ce da ba a taba gani ba. (Fa’iza Mustapha)














