Masana masana’antu sun yi kira ga daukar matakai gaggawa don dakatar da kaura kamfanoni masu zaman kansu ficewa daga daga Nijeriya zuwa kasashen waje, inda suka jaddada bukatar tsara cikakkun manufofin masana’antu da za su bunkasa bangarorin masana’antu, karfafa zuba jari na masu zaman kansu, da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin sassa daban-daban na tattalin arziki.
Masana masana’antun da suka zanta da LEADERSHIP Sunday sun jaddada muhimmancin jan hankali wajen Zuba Jari Kai Tsaye na Kasashen Waje (FDI) mai dorewa, wanda ya fi mayar da hankali kan ci gaban masana’antu da albarkatu fiye da samun kudade na dan gajeren lokaci.
- Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano
- Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe
Daraktan Janar na Kungiyar Masana’antu ta Nijeriya (MAN), Mista Segun Ajayi-Kadir, da shugaban Kungiyar Masu Kananan Harkokin Kasuwanci na Nijeriya (ASBON), Dakta Femi Egbesola, sun ce akwai bukatar kirkirar manufofin masana’antu da za su bunkasa ci gaban masana’antu a kasar.
Shugabannin masana’antu sun kuma yi kira ga gwamnati da ta daidaita tattalin arziki, inganta saukin gudanar da harkokin kasuwanci, da aiwatar da shirye-shiryen tallafi ga masana’antu na cikin gida.
Bugu da kari, masana sun nuna cewa rikicin kudin waje da rashin daidaito a kimar musayar kudi su ne manyan matsaloli ga kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen waje, inda kalubalen samun damar mayar da ribar kamfani zuwa kasashen waje da samun kudin waje ke rage amincewar masu zuba jari sosai kuma yana karfafa su su bar kasar.
Binciken da LEADERSHIP Sunday ta gudanar ya nuna cewa yanayin tattalin arzikin Nijeriya ya sha wahala tun daga shekarar 2020, inda wasu kamfanoni suka rufe ayyukansu, ko suka yi kaura, ko kuma suka rage yawan ayyukansu a kasar.
Ana danganta wannan yanayi da wahalhalun tattalin arziki, canje-canjen kimar kudi, da tsadar gudanar da ayyuka, wanda hakan ya haifar da asarar ayyukan yi da kuma rashin daidaiton tattalin arziki mai yawa.
Wasu daga cikin manyan kamfanonin da suka bar Nijeriya sun hada da Standard Biscuits Nigeria Limited, NASCO Fiber Product Limited, Union Trading Company Nigeria Plc, da Deli Foods Nigeria Limited.
Ficewar wadannan kamfanonin daga kasuwar Nijeriya ya samo asali ne daga tasirin rashin daidaiton tattalin arziki da sauran kalubalen gudanarwa.
Yawancin kamfanonin sun bayyana cewa matsalolin tattalin arziki masu tsanani, canje-canjen kimar kudi marasa tabbas, da hauhawar farashin gudanar da ayyuka su ne manyan dalilan da suka sa suka yanke wannan shawara.
“Nijeriya dole ne ta samar da tsarin da zai ja hankalin wadanda za su zuba jari a masana’antu, hakar ma’adanai, wadanda za su sarrafa albarkatun kasa da kayan albarkatun da ake da su, tare da tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai hadin kai,” in ji shi.
Haka kuma, shugaban Kungiyar Masu Kananan Harkokin Kasuwanci na Nijeriya (ASBON), Dakta Femi Egbesola, ya bayyana cewa ficewar kamfanoni masu zaman kansu na kasashen waje ya shafi yawancin Kananan da Matsakaitan Harkokin Kasuwanci (SMEs) da kamfanoni na cikin gida da ke aiki a kasar, tare da karawa da cewa gwamnati dole ne ta dauki matakan gaggawa don hana ficewar kamfanonin ketare.
A yayin da yake magana da daya daga cikin wakilanmu, Daraktan Gudanarwa na Cowry Asset Management Company, Johnson Chukwu, ya bayyana cewa haduwar rikicin kudin waje da rashin daidaito a kimar musayar kudi ya yi tasiri mara kyau ga ra’ayin masu zuba jari na kasashen waje wajen ci gaba da shiga harkokin zuba jari na kamfanoni masu zaman kansu a kasar.