• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masana Sun Dora Alhakin Rashin Cika Alkawuran ‘Yan Siyasa Kan Jam’iyyu

by Sani Anwar
3 weeks ago
Siyasa

Jam’iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula (CSOs) da manyan masana kimiyyar siyasa, sun bayyana damuwarsu cewa; matukar ba a magance matsalar rashin daidaito da akida wajen aiwatar da manufofin jam’iyyuba, babu shakka; ba za a iya samun ingantaccen shugabanci ba, musamman a jihohi.

Yayin zantawa da LEADERSHIP, sun zargi gazawar tsarin jam’iyyun siyasa a halin yanzu.

  • Ana Fatan Majalisar Wakilan Amurka Za Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Raya Hadin Gwiwar Sin Da Amurka
  • ’Yansanda Sun Kama ‘Yan Fashi A Kaduna, Sun Ƙwato Bindiga Da Wayoyi

Har ila yau, sun tuna da cewa; kowace jam’iyyar siyasa a jamhuriya ta biyu, tana da akida guda daya da kuma bayyanannen tsari, wanda gwamnatin jam’iyyar ta aiwatar a kowane mataki.

Sannan sun lura cewa, jam’iyyun siyasa a halin yanzu; ba su da akidar siyasa, kuma mambobinta ba su da da’a wajen aiwatar da tsarin nasu, hatta a jihohin da suke mulki.

Kazalika, sun koka kan yadda shugabannin kasa da gwamnoni suka kwace jam’iyyu, tun bayan komawar mulkin demokuradiyya a shekarar 1999, manazartan sun yi nuni da cewa; alkawuran da aka yi wa al’umma a lokacin yakin neman zabe, yanzu ya koma na jam’iyya.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan.

A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN.

Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin jam’iyyun UPN da PRP, a matsayin na masu fafutuka da kuma jajircewa, domin kuwa jam’iyyar UPN ta tsaya tsayin-daka wajen aiwatar da manufofinta.

An gina tsarin jam’iyyar bisa manyan manufofi hudu kamar haka: ilimi kyauta tun daga makarantar reno har zuwa manyan makarantu, harkar kiwon lafiya kyauta, hadin gwiwar karkara da ci gabanta da kuma samar da cikakkun ayyukan yi masu dorewa. Wadannan alkawura, an bi su ne bisa tsari na addini a jihohin da suka yi mulki, wato Jihar Legas, Oyo, Ogun, Ondo, da kuma Bendel.

A halin da ake ciki yanzu, yunkurin daidaita daidaito wajen aiwatar da tsarin ya samu matsala, a cewar rahoton LEADERSHIP.

LEADERSHIP ta tuna cewa, yunkurin da gwamnonin jihohi suka yi a baya na aiwatar da tsarin duba takwarorinsu a karkashin kungiyar gwamnonin Nijeriya, yanzu abin bah aka yake ba.

Yayin da jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP ke ci gaba da gudanar da taron gwamnoninsu, an nuna damuwa kan rashin aiwatar da muhimman tsare-tsaren jam’iyyar da kuma ci gaba da shirye-shiryen jam’iyyar ta hanyar gwamnatocin jam’iyyar daya da suka gaje su, wanda hakan ke haifar da manufofin jam’iyyar.

Wannan lamari dai ya kara yin tsamari sakamakon ficewar gwamnoni daga jam’iyyunsu.

Tun daga 1999, jam’iyyu sun zama tamkar wasu motoci ne da ake yin amfani da su, domin cin zabe;

 

Ba Za Mu Sake Bari Haka Ta Faru Ba – ADC

Sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya shaida wa LEADERSHIP cewa; rikicin da ke tattare rashin aiwatar da tsarin jam’iyyya na bai-daya a jihohin da jam’iyya daya ke mulki, na nuna cewa wata babbar matsala ce.

Ya ce, tun daga farkon jamhuriya ta hudu, jam’iyyu suka zama masu matukar rauni a cikin al’umma tare da kasancewa a matsayin wani dandali na ‘yan siyasa na tsayawa takara.

“Saboda haka, ba kamar jam’iyyun jamhuriya ta biyu ba, wadanda suka ginu a kan akidu, manufofi da kuma tsare-tsare. Jam’iyyun a wancan jamhuriyar, sun kasance tamkar wasu motoci na musamman, domin gudanar da zabe; saboda haka, don ba su da karfi; ba za su iya dora ikonsu ko akidunsu a kan daidaikun ‘yan siyasa ba.

“Don haka, idan kuna da jihohi shida a karkashin jam’iyya, sannan kuma kowannensu ya fitar da nasa tsarin ba tare da an ga akida daga jam’iyyar ba, to sai a ga irin wannan rashin jituwa, rabuwar kai ko kuma rashin jituwar ta yi yawa.

Ya kara da cewa, a jamhuriya ta biyu mutane sun zabi jam’iyyu ne saboda abin da za su samu.

“Shi yasa mutane irin su marigayi Chinua Achebe, sun shiga jam’iyyar PRP, saboda imani da ya yi da akidu da kuma manufofinta.”

“Amma ida za a iya tunawa, shugaban jam’iyyar ADC na kasa Sanata Dabid Mark ya ce; muna gina wannan jam’iyya ne, wanda ba za ta bar duk wanda aka zaba a ADC ya yi abin da ya ga dama ba bayan samun mulki. Daga rana ta farko, za mu mika wa zababbu manufofin da ke kunshe da wannan jam’iyya,” in ji shi.

Ya ce, idan har jam’iyyu za su iya bunkasa tsarin tafiyar da harkoki da manufofinsu na al’umma, duk wanda ya samu mukami dole ne ya aiwatar da manufofin jam’iyya, kamar yadda aka gani a jamhuriya ta biyu a karkashin jam’iyyar UPN.

Ya yi nuni da cewa, babbar mafita ita ce karfafa jam’iyyun siyasa tare da tabbatar da cewa; ba za su bison zuciyar mutane ba.

 

Dalilin Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Kasa Aiwatar Da Manufa Iri Daya- IPAC

Majalisar bayar da shawara kan jam’iyyu (IPAC), ta bayar da haske kan dalilan da suka haifar da wannan gazawa ta demokuradiyya tare da samar da hanya mai bullewa.

A wata tattaunawa da LEADERSHIP, shugaban IPAC na kasa, Dakta Yusuf Mamman Dantalle ya bayyana cewa; manufofin jam’iyya, wadanda ke tattare da akidu da manufofin da ke tsakanin jam’iyyun siyasa da masu zabe, sun zama tamkar wadansu takardu da ake yin watsi da su bayan kammala zabe.

Duk da haka, shugaban na IPAC ya lura cewa; fassarar alkawuran da aka yi a sakamakon gudanar da mulki, ya zama mai matukar wahala; saboda dalilai da dama, ciki har da inganta yanayin zamantakewa da tattalin arziki, banbancin da ke tsakanin jihohi da kuma na kananan hukumomi.

 

Akwai Bukatar Sauya Fasalin Tsarin Cikin Gaggawa – CISLAC

Da yake zantawa da LEADERSHIP kan wannan batu, babban jami’in tsare-tsare a cibiyar CISLAC, Suleiman Gimba ya nuna cewa; demokuradiyyar Nijeriya na fama da matsananciyar matsala, rashin daidaito, musamman wajen aiwatar da manufofin jam’iyya.

Ya bayyana yadda a baya aka taba kafa tsarin mulkin siyasa a karkashin jam’iyyu irin su UPN, wanda a halin yanzu abubuwan ba haka ake gudanar da su ba.

“Gwamnonin da aka zaba a jam’iyya guda, suna bin wasu manufofi daban-daban, wasu jihohin sun tafi a bangaren samar da ababen more rayuwa, wasu sun tafi a kan wasu abubuwa da ban, wasu kuma ma babu ruwansu da akidar da jam’iyyar tasu ta kafu a kai,” in ji Gimba.

“Dalili kuwa shi ne, saboda a yau; jam’iyyun suna aiki ne tamkar wasu na’urorin lashe zabe fiye da gwamnati.”

Gimba ya dora alhakin hakan a kan wasu muhimman abubuwa guda uku: raunin tsarin jam’iyya na cikin gida, rashin tushen akida da kuma rashin tsarin samar da kudade ga jam’iyyun siyasa.

A cewar tasa, idan ba tare da tallafin jama’a ko samar da wata hanyar shigowar kudade mai dorewa ba, jam’iyyu za su ci gaba da yin garguwa da masu hannu da shuni da kuma masu rike da madafun iko ne, wadanda ke bankado ayyukansu.

Gimba ya kara kwatanta shugabannin Nijeriya da alakarsu da jam’iyyun siyasa.

Ya ce, Obasanjo ya nuna karfi tare da juya jam’iyyarsa yadda yake so a lokacin mulkinsa, inda su ma shugabannin da suka biyo bayansa ke ci gaba da kwatanta hakan.

Kazalika, ya kawo misali da ajandar Tinubu ta ‘Renewed Hope Agenda’, wanda ya bayyana shirin a matsayin nasa na kashin kansa, maimakon na tsarin jam’iyyar APC.

“Babu shakka, wannan sauyi ya ci gaba da raunana jam’iyyun siyasa, yanzu haka muna da shugabannin zartarwa da ke mulki ta hanyar ka’idojin kashin kansu tare da kawar da akidun jam’iyya baki-daya, in ji shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
Rahotonni

Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya

October 11, 2025
Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
Rahotonni

Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki

October 11, 2025
Next Post
Hadin Tsumin Baure

Hadin Tsumin Baure

LABARAI MASU NASABA

Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

October 20, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta

October 20, 2025
Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

October 19, 2025
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025
Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

Ƴansanda Sun Kama Ɗan Jarida A Kano Bisa Zargin Ɓata Suna

October 19, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.