Daya daga cikin wadanda aka assasa babbar masana’antar nishadi da ke amfani da harshen Hausa wajen isar da sako a fadin Duniya wadda ake wa lakabi da Kannywood kuma ta ke da matsugini a babban birni mai tarihi wato Kano,Tahir Fagge ya ce masana’antar a yanzu ta sauka daga kan turbar da tun farko aka gina ta akai.
Jarumin a wata hira da ya yi ya ce tun farko an gina masana’antar a kan wasu manyan tubali da suka hada da kaunar juna, shawarwari da kuma shugabanci nagari, amma yanzu an rasa wasu daga cikinsu saboda zuwan zamani da sauran dalilai.
- Ban Hadu Da Wani Kalubale A Lokacin Shiga Masana’antar Kannywood Ba -Fiddausi Yahaya
- Matsalar Tsaro: Matawalle Ya Ziyarci Jihar Zamfara
Tahir ya ce a baya duk wani dan Kannywood ya na matukar ganin dan uwansa ya samu karuwa idan kuma wata matsala ta faru dashi, zai jajanta mashi sannan idan akwai wani taimako da zai iya yi wajen fitar wannan damuwar zai yi ba kamar yanzu da kowa kanshi ya sani ba.
A zamanin baya idan wani zai shirya fim zai kawo labarin fim din a gaban manya a cikin masana’antar sai a duba a gani idan akwai wani gyara a yi idan kuma babu gyara sai a bashi shawarwarin da suka dace, sannan a baya akwai zumunci mai karfi a tsakanin wadanda ke cikin masana’antar, amma zuwan wayoyin hannu ya sa sai dai mutum ya kiraka a waya ya yi maka murna ko ya jajanta maka ba tare da ya zo har inda kake ba inji shi.
Dangane da shigowar manhajar YouTube da sauran shafukan yanar gizo inda ake dora fina finai a maimakon faifan cd da ake yi lokacin baya, Fagge ya kira wannan abu da ci gaban mai hakar rijiya domin kuwa ya na yin kasa ya na cewa an samu ci gaba.
Idan kuka lura a baya mutum ya kan cire kudmdi kalilan ya yi fim dinsa mai kyau ya tafi kasuwa ya sayar ya samu riba mai yawa ba tare da wata tangarda ba, amma yanzu sai ka zuba makudan kudade wajen neman mabiya a shafukan yanar gizo wadanda za su dinga kallon fina finanka da kake dorawa lokaci bayan lokaci sannan ne za ka samu wani abin kirki.
Da aka tabo batun yadda wani lokaci a baya aka gane shi a wani waje wanda ake kyautata zaton gidan rawa ne kokuma gidan solo kamar yadda wasu suka sani, kuma har ta kai ga wadansu na ganin bai dace babban mutum kamar shi ya tafi irin wadannan wuraren da aka sani mafi yawancin wadanda ke wajen matasa ne da suka tafi domin a nishadantar dasu ba.
Tahir Fagge ya ce zuwa gidan solon da aka gani ya je ba haka kawai ya tafi ba, domin kuwa an iske shi har gida aka nemi ya tafi a matsayin babban bako a wurin wanda a wancan lokacin yake sabon budewa, bayan ya tafi ne kuma suka bukaci ya nishadantar da wadanda ke wajen kuma a matsayinsa na jarumi kuma wanda yake da masoya sai ya ga idan yaki ba za su ji dadi ba.
Bayan an saka wata wakar da a wajen aka rasa wanda zai iya taka rawar ta, duba da cewa tsohuwar waka ce sai ya yi zumbur ya tashi ya taka rawa domin ya nunawa matasan da ke wajen cewa da tsohuwar zuma ake magani, hakan ya sa mahukuntan wajen su ka ji dadi har suka yi mashi kyautar manyan kudade wanda a wannan lokacin yake da matukar bukatar kudi domin tafiya neman magani in ji shi.