Sabuwar jaruma a masana’antar Kannywood Fiddausi Yahaya wadda yanzu haka ta fito a manyan fina finai da suka hada da Labarina da Garwashi ta bayyana yadda ta samu shiga masana’antar Kannywood cikin sauki ba tare da wata wahala kamar yadda wasu ke samu ba.
Fiddausi yayin da ta ke hira da manema labarai ta ce tun a kuruciya ta ke sha’awar shiga wannan harka ta fim amma ba ta nuna hakan ga yan uwa da abokan arziki ba sai yanzu, kuma cikin ikon Allah bayan ta nuna ra’ayin nata na shiga harkar kuma ta samu goyon baya daga iyayenta.
- Kungiyar Masu Masana’antu Ta Samu Bashin Naira Biliyan 75 Daga Bankin BOI
- Kashi 4.1 Na ‘Yan Nijeriya Ne Kawai Za Su Amfana Da Tsarin Mafi Karancin Albashi —Bankin Duniya
Ta ce tun ba yanzu ba na ke sha’awar shiga Kannywood amma ban sanar a gidanmu ba saboda haka da na samu zuwa Kano kuma na nuna sha’awar harkar sai aka bukaci in fara magana da gida domin kafin su saka jarumai mata a cikin fim dole ana bukatar sahalewar iyaye, haka kuwa aka yi na kira iyayena da sauran wadanda su ka isa dani kuma suka amince mani in fara da kuma yi mani fatan alheri.
Dangane da kalubalen da wasu ke fuskanta yayin shiga masana’antar Kannywood Fiddausi ta ce ko kusa ko alama ba ta hadu da wannan kalubalen ba,cikin aminci na fara wannan harka kuma yanzu cikin ikon Allah na fito a manyan fina-finai, in ji ta.
A kan nasarori kuwa Fiddausi wadda ta ce yar asalin Sakkwato ce ta bayyana cewar babu wata nasara a rayuwa da ya wuce ka nemi abu kuma ka samu,don haka babbar nasarar da ta samu a wannan masana’antar shi ne samun abinda ta ke sha’awa domin kuwa ba kowane mutum ne ya ke samun abinda ya bukata kuma a lokacin da ya bukaci wannan abin ba.
Don haka Fiddausi ta ce wannan kadai babbar nasara ce a nata ganin,daga karshe jatumar ta yi godiya da dimbin masoyanta kuma ta yi masu fatan alheri inda ta roki Allah da ya kara dankon kauna a tsakaninsu.