Ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ta bayyana cewa, sashen kera bayanan kayayyakin laturoni na kasar Sin ya samu bunkasuwa sosai a fannin fitar da kayayyaki, da hada-hadar kudaden shiga da riba a watanni biyar na farkon shekarar 2024.
Bayanai sun nuna cewa yawan kayayyakin da manyan kamfanoni na wannan fannin suka samar ya karu da kashi 13.8 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin na bara.
- Nijeriya Ta Ƙarƙare Yarjejeniyar Haɗin Guiwa Da Kamfanin Jiragen Sama Na Ethiopia
- An Kafa Tashar Adana Narkakkiyar Iskar Gas Mafi Girma A Kasar Sin
Adadin kudaden shiga na manyan kamfanoni na wannan fanni ya karu da kashi 8.5 cikin 100 zuwa yuan tiriliyan 5.95 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 834.88 idan aka kwatanta da makamancin lokacin na bara, kuma ribar da wadannan kamfanoni suka samu ya karu da kashi 56.8 cikin dari zuwa yuan biliyan 194.6.
Manyan kamfanonin da ke wannan fanni su ne wadanda ke da manyan kudaden shiga na kasuwanci na shekara-shekara na a kalla yuan miliyan 20. (Mai Fassara: Mohammed Baba Yahaya)