Alkaluman hukuma sun nuna cewa, masana’antar samar da wutar lantarki bisa karfin hasken rana na kasar Sin, ta samu ci gaba matuka a shekarar 2022, inda adadin kudin da masana’antar ke samarwa ya haura kudin Sin RMB yuan triliyan 1.4, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 203.9,
Manyan hanyoyin samar da kayayyaki na masana’antar, ciki har da polysilicon, wafers, cell da sauran kayayyaki, duk sun habaka kan na shekarar 2021 da kusan sama da kashi 55 bisa kashi 100, a cewar ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin.
A shekarar 2022 da ta gabata, kasar Sin ta ci gaba da gina manyan sansanonin samar da farantar dake samar da wutar lantarki bisa karfin hasken rana da amfani da faranta da aka rarraba, inda karfin sabbin farantan da kasar ta kafa suka kai gigawatts 87.
Bayanai na nuna cewa, karfin bukatun kasuwanni na ketare a fannin sabbin makamashi, ya kara yawan farantan da kasar Sin take fitarwa zuwa ketare. Darajar farantar samar da wutar lantarki bisa karfin rana da kasar Sin ta fitar zuwa ketare, ta kai dalar Amurka biliyan 51.2 a bara.
A cewar ma’aikatar, a shekarar 2022, makamashin da ake iya sabuntawa da kasar Sin ta samar, ya yi daidai da raguwar hayakin carbon dioxide da ya kai tan biliyan 2.26 a cikin gida.(Ibrahim)