A karon farko, kasar Sin ta kaddamar da wata sabuwar tashar samar da lantarki daga hasken rana da karfin igiyar ruwa, wadda ke da karfin samar da lantarkin da ya zarce kilowatt miliyan 100 cikin shekara guda.
Hakika wannan wani karin nasara ce ga kasar Sin a kokarin da take ci gaba da yi na rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli. Haka kuma nasara ce ga duniya domin ta gabatar musu wani abun misali da koyi a bangaren amfani da makamashi mai tsafta domin raya muhalli da biyan bukatun al’umma.
Abun da ya burge ni cikin wannan sabuwar fasaha shi ne, yadda aka hada hasken rana da karfin igiyar ruwa. Wato za a samu makamashi a lokacin da rana ta kwalle daga haskenta, yayin da idan dare ya yi, za a samu makamashi daga karfin igiyar ruwa, ta yadda a ko da yaushe, ba za a raba rasa makamashi ba. Ba shakka, masanan kasar Sin na ci gaba da gabatar da sabbin abubuwa na ban mamaki masu ma’ana da aminci ga al’ummar duniya.
Duk da irin ci gaban da Sin ta samu, har yanzu ba ta gajiya ba, tana kara kokarin kirkiro sabbin fasahohi da nufin biyan bukatun al’ummarta, lamarin dake ci gaba da nuna yadda walwalar al’ummarta ke kasancewa kan gaba a cikin manufofinta. Misali, wannan tasha za ta biya bukatar lantarki na gidaje kimanin 30,000 na birnin Wenling dake lardin Zhejiang.
Hasken rana da igiyar ruwa, albarkatu ne da kowacce kasa ba za ta rasa ba, musamman ma kasashenmu na Afrika. La’akari da yadda ake fama da rashin lantarki a kasashen, kamata ya yi su kara kyautata huldarsu da kasar Sin domin koyon dabarunta.
Kasar Sin ita ce mafi yawan al’umma a duniya, amma duk da haka, al’ummarta na cikin walwala saboda jajircewarta. A ganina, sauran kasashe masu tasowa ba su da wani dalili na rashin kyautata walwalar al’ummarsu. Ya kamata ci gaban kasar Sin ya zama mai ba su kwarin gwiwa.