“Taruka biyu”, wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar (CPPCC) da har yanzu ke gudana a birnin Beijing, na jawo hankulan kasashen duniya. Rahoton aikin gwamnatin kasar Sin na shekarar 2024, ya gabatar da karfafa aikin gina tsarin masana’antu na zamani, da kuma hanzarta raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko.
Wani masani dan Najeriya Samson Ibiang ya bayyana a wata hira da manema labarai kwanan nan, cewa kasar Sin na daya daga cikin manyan kasashen da ke taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya. Raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko ba kawai kasar Sin za ta amfana ba, har ma da sauran kasashe masu tasowa na duniya.
A cewarsa, yana da matukar muhimmanci ganin yayin da kasar Sin ke neman samun ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire da sauran hanyoyin samar da kayayyaki, ba za ta kuma kyale hakikanin halin da ake ciki a larduna da yankuna daban-daban na kasar ba. Sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko ba wai kawai suna da amfani ga kasar Sin ba, har ma da sauran kasashe masu tasowa na duniya. Kar a manta cewa, kasar Sin na daya daga cikin manyan kasashen da ke ba da gudummawa ga tattalin arzikin duniya, kuma irin dabarun ci gaba da Sin ta dauka za su yi babban tasiri. (Mai fassara: Bilkisu Xin)