Babban jami’in tattalin arziki na MDD Hamid Rashid ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a wata hira da aka yi da shi bayan wallafa rahoto game da yanayin tattalin arzikin duniya da hasashen da ake yi a shekarar 2023 cewa, kasar Sin za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen karfafa ci gaban duniya a shekarar 2023.
A cewar Rashid dake zama shugaban sashen sanya ido kan tattalin arzikin duniya, da nazarin tattalin arziki da siyasa da zamantakewa na MDD, shekarar 2022 shekara ce mai wahalar gaske, amma a shekarar 2023, kasar Sin za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga ci gaban duniya, yayin da yake karin haske kan makomar tattalin arzikin kasar Sin. Ya ce, ya yi imani tare da kyakkyawan fatan cewa, abubuwa za su farfado a kasar Sin.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai samu murmurewa mai karfi a shekarar 2023, yayin da manufofinta suke bisa hanya, ma’ana manufar kasafin kudi da kuma tsarin kudi na kasar, duk suna kan hanyar da ta dace.
Rashid ya ce, tattalin arzikin kasar Sin yana da kyakkyawan muhalli wajen samun ci gaba, saboda hauhawar farashin kayayyaki ta ragu, idan aka kwatanta da hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a wasu kasashe, kuma hakan wata babbar dama ce.(Ibrahim)