A jiya ranar Litinin, Kagiso Pooe, wani babban malami a makarantar koyon harkar shugabanci ta Witwatersrand ta kasar Afirka ta Kudu ya bayyana cewa, a cikin shekaru 25 da suka wuce, dangantakar da ke tsakanin kasashen Afirka ta Kudu da Sin ta samu ci gaba sosai a fannonin cinikayya, siyasa, da mu’amalar jama’a, wadda ta haifar da moriyar juna ga bangarorin biyu.
Kasar Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayyar Afirka ta Kudu tun daga shekarar 2009, kuma kasar Afirka ta Kudu ta kasance babbar abokiyar cinikayyar kasar Sin a Afirka tun daga shekarar 2010. Idan aka yi la’akari da nan gaba, akwai yiwuwar Afirka ta Kudu ta kara yawan mu’amalar cinikayya da kasar Sin, musamman wajen fitar da kayayyakin amfanin gona zuwa kasashen waje.
Dangantakar kasashen biyu ta samu bunkasuwa, idan muka dauki mu’amala tsakanin jama’ar kasashen biyu a matsayin misali, dimbin daliban Afirka ta Kudu ke zuwa kasar Sin don yin karatu a fannin injiniya da likitanci, kuma da alama hakan zai ci gaba, in ji Pooe.
Ya ce, a yayin da kasashen biyu ke bikin cika shekaru 25 da kulla huldar diflomasiyya, akwai abubuwa da dama da aka shirya gudanarwa a Afirka ta Kudu a duk wannan shekara. (Mai fassarawa: Yahaya)