A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne.
Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin manufofinta na tattalin arziki. Sai dai a daya hannun, kasar Sin na kara fadada bude kofarta.
Ya ce Amurka na ingiza salon rufe fasahohinta, yayin da Sin ke kara gabatarwa duniya da fasahohin ci gaba. Dukkanin wadannan na nufin Sin za ta zamo mai cin gajiya daga bunkasar tattalin arzikin duniya a shekaru masu zuwa. Daga nan sai mista Jeffrey ya nuna damuwa game da halin da Amurka ke ciki, yana mai cewa manufofin gwamnatin Trump ba su da ma’ana ga Amurka ita kan ta da ma duniya baki daya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp