• English
  • Business News
Saturday, August 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masanin Huldar Kasa Da Kasa A Jami’ar Abuja: Kasar Sin Na Sa Kaimi Ga Sabon Nau’in Dunkulewar Duniya

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Masanin Huldar Kasa Da Kasa A Jami’ar Abuja: Kasar Sin Na Sa Kaimi Ga Sabon Nau’in Dunkulewar Duniya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shugaban sashen ilimin siyasa da huldar kasa da kasa a jami’ar birnin Abuja dake tarayyar Najeriya Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, ya ce kasar Sin ta ba da gudummawa mai kyau, ga sabon nau’in tsarin dunkulewar duniya, da gudanar da harkokin mulki a duniya, kuma tana daya daga cikin masu sa kaimi ga sabon tsarin duniya.

Sheriff Ghali Ibrahim, ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da manema labarai a baya-bayan nan.

  • Ya Wajaba Amurka Ta Kaucewa Sake Maimaita Irin Kuskuren Da Ta Aikata Game Da Taiwan

Shaihun malamin ya ce an dade ana aiwatar da dunkulewar duniya, bisa jagorancin kasashen yamma, da nufin inganta tsarin siyasa, da tsarin tattalin arziki, da akidu, da al’adu irin na kasashen yamma a duk fadin duniya, domin cin gajiyar dukkanin duniya, kuma yawancin kasashen Afirka, da sauran kasashe masu tasowa, ba sa iya cin gajiyar irin wannan tsari na dunkulewar duniya.

Dangane da maganar “raba gari da kasar Sin ta fannin tattalin arziki”, da wasu cibiyoyi da ‘yan siyasar yammacin duniya suka kira a yi a baya-bayan nan, Farfesa Ghali ya yi nuni da cewa, hakan na faruwa ne, kawai saboda ba za su amince da cewa, kasar Sin na samun bunkasuwa cikin sauri ba, kuma suna fargabar cewa, nasarar da Sin ta samu za ta zama abin koyi ga sauran kasashe masu tasowa, wanda hakan zai girgiza ikonsu na mallakar moriyar duniya.

Farfesa Ghali ya kara da cewa, shigar da kasar Sin cikin tsarin samar da kayayyaki na duniya, muhimmin taimako ne ga ci gaban tattalin arzikin kasashe masu tasowa irinsu Najeriya, kuma shawarar “Ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar, na ci gaba da taimakawa kasashe masu tasowa, wajen inganta ababen more rayuwa da ake bukata, domin samun ci gaba.

Labarai Masu Nasaba

Xi Jinping Ya Zanta Da Putin Ta Wayar Tarho

Shin Amurka Ta Manta Da Azabar “Babban Koma-Baya” Tare Da Haraji Mafi Yawa a Lokacin Na Tsawon Kusan Karni?

Kaza lika babbar kasuwar kasar Sin da ke bude kofa ga kasashen waje, tana da matukar jan hankalin kasashe masu tasowa.

Ghali ya jaddada cewa, maganar “raba gari da kasar Sin ta fannin tattalin arziki”, ba za ta samu amincewa daga kasashe masu tasowa ba, saboda hakan na nufin raba gari da samun ci gaban su.

A cewar masanin, “Idan babu kasar Sin, ba za a samu zarafi na ci gaba da yunkurin dunkulewar duniya ba”. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Launukan Kawata Falo Masu Ban Sha’awa (2)

Next Post

Na Fuskanci Kalubale Daga Mutanen Da Har Yanzu Ba Su Fahimci Fim Ba –Ibrahim Gungu

Related

Xi Jinping Ya Zanta Da Putin Ta Wayar Tarho
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Zanta Da Putin Ta Wayar Tarho

18 hours ago
Shin Amurka Ta Manta Da Azabar “Babban Koma-Baya” Tare Da Haraji Mafi Yawa a Lokacin Na Tsawon Kusan Karni?
Daga Birnin Sin

Shin Amurka Ta Manta Da Azabar “Babban Koma-Baya” Tare Da Haraji Mafi Yawa a Lokacin Na Tsawon Kusan Karni?

19 hours ago
Sin Ta Mika Sabon Kason Tallafin Abinci Ga Zimbabwe
Daga Birnin Sin

Sin Ta Mika Sabon Kason Tallafin Abinci Ga Zimbabwe

20 hours ago
An Bude Taron Mutum-Mutumin Inji Na Duniya Na 2025 A Yau Juma’a
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Mutum-Mutumin Inji Na Duniya Na 2025 A Yau Juma’a

21 hours ago
Sin Ta Gabatar Da Korafi Da Babbar Murya Dangane Da Kalaman Jagoran Philippines 
Daga Birnin Sin

Sin Ta Gabatar Da Korafi Da Babbar Murya Dangane Da Kalaman Jagoran Philippines 

22 hours ago
Xi Ya Bukaci A Yi Dukkan Mai Yiwuwa Wajen Gudanar Da Ayyukan Bincike Da Ceto Bayan Aukuwar Ambaliya A Lardin Gansu
Daga Birnin Sin

Xi Ya Bukaci A Yi Dukkan Mai Yiwuwa Wajen Gudanar Da Ayyukan Bincike Da Ceto Bayan Aukuwar Ambaliya A Lardin Gansu

23 hours ago
Next Post
Na Fuskanci Kalubale Daga Mutanen Da Har Yanzu Ba Su Fahimci Fim Ba –Ibrahim Gungu

Na Fuskanci Kalubale Daga Mutanen Da Har Yanzu Ba Su Fahimci Fim Ba –Ibrahim Gungu

LABARAI MASU NASABA

Man United Sun Kammala Sayen Benjamin Sesko Daga RB Leipzig

Man United Sun Kammala Sayen Benjamin Sesko Daga RB Leipzig

August 9, 2025
An Naɗa Farfesa Adamu Muƙamin Mataimakin Shugaban Jami’ar Yakubu Gowon, Abuja

An Naɗa Farfesa Adamu Muƙamin Mataimakin Shugaban Jami’ar Yakubu Gowon, Abuja

August 9, 2025
Gwamnan Kano Ya Sallami Mataimaka Biyu Kan Zargin Karkatar Da Kayan Tallafi

Gwamnan Kano Ya Sallami Mataimaka Biyu Kan Zargin Karkatar Da Kayan Tallafi

August 9, 2025
Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu

Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu

August 9, 2025
Ina Fatan Taka Inda Yayana Ya Taka A Fagen Ƙwallon Ƙafa A Duniya -Jobe Bellingham

Ina Fatan Taka Inda Yayana Ya Taka A Fagen Ƙwallon Ƙafa A Duniya -Jobe Bellingham

August 9, 2025
Sai An Magance Matsalar Asusun Haɗin Gwiwa, Za A Tabbatar Da Cin Gashin Kan Ƙananan Hukumomi

Sai An Magance Matsalar Asusun Haɗin Gwiwa, Za A Tabbatar Da Cin Gashin Kan Ƙananan Hukumomi

August 9, 2025
Tinubu Ya Gwangwaje Ƴan Wasan Ƙwallon Kwando Ta Mata Da Dala $100,000 Kowace

Jerin Ƴan Wasa Mata Da Suka Samu Kyautar Dala 100,000 Daga Gwamnatin Nijeriya

August 9, 2025
Afrika Ba Ta Cikin Jerin Fannonin Da Muke Ba Fifiko – Amurka

Afrika Ba Ta Cikin Jerin Fannonin Da Muke Ba Fifiko – Amurka

August 9, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 9 A Kogi

Ƴan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 9 A Kogi

August 9, 2025
ADA/ADC, APC Da PDP: Jam ’iyyun Siyasa Da Ke Shan Jinin ’Yan Nijeriya

ADA/ADC, APC Da PDP: Jam ’iyyun Siyasa Da Ke Shan Jinin ’Yan Nijeriya

August 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.