• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Masanin Masar: Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Wani “Karfi Ne Dake Ingzia Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka

by CMG Hausa
3 years ago
Masar

Wani mai sharhi kan harkokin siyasa na kasar Masar ya bayyana cewa, shawarar ziri daya da hanya daya, ta ingiza kokarin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, duba da irin gudummawar da shawarar ta bayar ga ci gaban Afirka.

Ezzat Saad, darektan hukumar kula da harkokin waje ta Masar, shi ne ya bayyana hakan, yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua da aka yi da shi a baya-bayan nan, yana mai cewa, galibin kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Afirka, ciki har da Masar, abokan hadin gwiwar shawarar ce, kuma shawarar ta samar da alfanu da dama ga nahiyar Afirka, ciki har da inganta ababen more rayuwa a kasashen Afirka.

  • Gobara Ta Ci Rayukan Mutum 41 A Wani Coci A Masar

Saad ya ce, sabanin tallafin da wasu kasashen yammacin duniya ke bayarwa, wadanda galibi suka takaita ga taimakon raya kasa bisa wasu sharudda da suke gindayawa, akwai bambanci mai girma da taimakon da kasar Sin ke baiwa kasashen Afirka.

Ya kara da cewa, kasar Sin ba ta gindaya wasu sharudda, kuma tallafin da take bayarwa, na da nufin yakar talauci da samun ci gaba ga kasashen Afirka.

Ya kuma ci gaba da cewa, hakika kasar Sin ta ba da babban taimako dangane da tsare-tsare na samun ci gaba a kasashen Afirka da dama.

LABARAI MASU NASABA

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Saad ya yi imanin cewa, shawarar ta kunshi dukkan sassan da za su shafi kyakkyawar dangantaka tsakanin bangarorinta, kuma tana yin hulda da bangarorin da suka hada da hadin gwiwar tattalin arziki, da ababen more rayuwa, da sufuri, da mu’amalar cinikayya, da zamanantar da fasahar zamani, da masana’antu, da goyon baya da musayar al’adu.(Ibrahim)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai
Daga Birnin Sin

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka
Daga Birnin Sin

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Next Post
Dangantaka Ta Yi Tsami Tsakanin Kwankwaso Da Shekarau

Dangantaka Ta Yi Tsami Tsakanin Kwankwaso Da Shekarau

LABARAI MASU NASABA

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025
Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

November 3, 2025
Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.