Shugaban kwamitin kwararru kan yaki da annobar COVID-19 na hukumar lafiya ta kasar Sin (NHC), Liang Wannian, ya fada a yau Alhamis cewa, kusan an kawo karshen COVID-19 a kasar Sin, amma ba a “kammala gaba daya ba” saboda har yanzu ana samun masu kamuwa da cutar jefi-jefi.
Annobar COVID-19 dai ta zama batun lafiyar gaggawa ta duniya, tun bayan da hukumar lafiya ta duniya ta ayyana ta a cikin shekarar 2020.
Liang ya bayyana a yayin wani taron manema labarai da kungiyar hadin gwiwa dake kandagarki da hana yaduwar cutar ta majalisar gudanarwar kasar ta gudanar cewa, “Ta bangare duniya, har yanzu yanayin cutar na ci gaba da wanzuwa, kuma har yanzu illar da cutar take yi na nan.” (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp