Masanin OECD: Karuwar Tattalin Arzikin Sin Na Inganta Bunkasuwar Tattalin Arzikin Duniya

Daga CRI Hausa

Jiya Alhamis, hukumar kididdigar kasar Sin ta fidda bayanin dake cewa, cikin farkon rabin shekarar bana, GDPn kasar ya karu da kaso 12.7 bisa dari.

Dangane da wannan batu, shugabar ofishin nazarin manufofin kasar Sin a kungiyar hadin gwiwa da raya tattalin arzikin duniya ta OECD Margit Molnar ta bayyana cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin yanayin zaman karko, zai inganta bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.

Ta ce, adadin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya yi daidai da hasashen da kungiyar OECD ta yi, kan yanayin karuwar tattalin arzikin kasar Sin a karshen watan Mayu na bana, inda ta ce, tattalin arzikin kasar Sin yana bunkasuwa cikin yanayin karko.

Ta kuma kara da cewa, bisa hasashen da kungiyar OECD ta yi, a bana, adadin karuwar tattalin arzikin duniya zai kai kashi 5.8 bisa dari, kuma, kasar Sin za ta samar da gudummawar kashi 1.58 bisa dari a wannan fanni.

Ma’anar hakan ita ce, karuwar tattalin arzikin kasar Sin zai samar da gudummawar kashi 27 bisa dari, cikin karuwar tattalin arzikin duniya. Hakan dai na shaida cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin cikin yanayin karko, zai inganta bunkasuwar tattalin arzikin yankin, da kuma na kasashen duniya baki daya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

Exit mobile version