Wani masanin tattalin arziki dan kasar Angola ya bayyana cewa, kasar Sin ce jigon ci gaban tattalin arzikin duniya, sakamakon gagarumin ci gaban da ta samu a fannin kimiyya, da fasaha, da kirkire-kirkire, da karfin fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare.
Darektan cibiyar nazari da bincike na jami’ar Katolika ta Angola, Manuel Jose Alves da Rocha, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, babu wata kasa da za a kwatanta ta da kasar Sin a fannin tattalin arziki.
Ya ce, ya kamata binciken da ake gudanarwa kan tattalin arzikin kasar Sin ba kawai ya mayar da hankali kan bayanan tattalin arzikin da aka samu a shekarar da ta gabata ba, har ma a kan yanayin ci gaban da ake samu. Yana mai cewa, kasashen Afirka ciki har da Angola, za su iya koyi da tsarin kasar Sin, fiye da lamuni da tallafin da kasar Sin din ke bayarwa. (Ibrahim Yaya)