ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gudu Zuwa Kasashen Waje: Gwamnati Na Shirin Taka Wa Likitoci Birki

by Idris Aliyu Daudawa
3 years ago
Likitoci

Yayin da yawan ‘yan Nijeriya ke karuwa kullum sai ga shi kuma kwararrun ta banagen kiwon lafaiya suna kara raguwa,saboda kuwa yadda tsarin kula da marasa lafiya yakamata ya kasance kamar yadda kudurin hukumar lafiya ta duniya ya bayyana na Likita  daya ya lura da marasa lafiya 1,000 yanzu al’amarin ya kasance ne na likita 1 ya duba marasa lafiya 10,000 a Nijeriya

Yadda kwararrun da suka shafi kula da lafiyar al’umma suke barin Nijeriya hakan ba karamin cikas yake kawo ma bangaren kula da lafiyar al’umma ba, yanzu kalilan wadanda kware a bangaren kula da lafiyar al’umma suke rage a Nijeriya,domin su kula da lafiyar ‘yan Nijeriya.

  • Sallah: Gwamna Bagudu Ya Umarci A Biya Albashin Watan Afrilu
  • INEC Ta Raba Muhimman Kayyayakin Zabe Don Kammala Zaben Gwamnan Kebbi

Alkalumman da ake dasu sun nuna Nijeriya ta rasa fiye da Likitoci 9,000 da suka barta zuwa kasashen Ingila, Kanada, da kuma Amurka tsakanin shekarun 2016 da 2018.Hakanan ma Likitoci 727 wadanda suka kware a Nijeriya suka koma Ingila kadai cikin wata shida, tsakaniu watannin Disamba  2021 da Mayu 2022.

ADVERTISEMENT

Alkalumman da aka samu daga cibiyar kula da aikin Nas da Unguwar zoma ta Ingila ta nuna ‘yan Nijeriya da aka koya masu suka kware daga aikin, ya nuna wadanda suke barin sun karu da kashi  68.4 ko daga2,790 a watan Maris na 2017 zuwa 7,256  na watan Maris 2022.”

Da yake tabbatar  da hakan  shugaban kungiyar Likitoci na kasa (MDCAN),yace bada dadewa ba Nijeriya tana daukar kawi Likitoci kashi 30 na 4000 da ake yayewa ko wace shekara a Nijeriya.Kamar yadda shugaban na kungiyar ta Likitoci, Doctor Bictor Makanjuola cewa yayi, “Muna daukar kashi 30 daga cikin wadanda muka sake horarwa 4,000 ko wace shekara”

LABARAI MASU NASABA

Sana’ar Kilishi:Yadda Ta Bunkasa Daga Jihar Katsina Zuwa Wasu Sassan Nijeriya

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

Makanjuola ya ce muna daukar kashi 30 na kwararru wadanda muke sake horarwa duk da yake Nijeriya ta sake shiga cikin matsalar za kuma ta cigaba da fuskantar hakan, har sai idan an dauki matakan daya kamata.

Ya kara jaddada cewa “Idan muka dauki kashi 30 na 12,000 hakan shi yafi fiye da kashi na4,000.idan kuma muka horar dai 12,000,kashi 30 shi yafi kyau fiye da wadanda ake dasu a halin yanzu na kusan 4,000.Da hakan mu kesa ran taimaka ma shi al’amarin ba kamar yadda ya dace ba amma a kalla dai ana cigaba da yin tsarin.”

Halin da ake ciki yanzu dokar hana hana Likitoci da Likitocin Hakora barin Nijeriya ta tsallake karatu na biyu a zaman majalisarWakilai ta kasa, har sai sun yi shekara biyar.

Kudurin dokar wanda Ganiyu Abiodun Johnson ya gabatar mai taken, “ Kuduri mai niyyar ayi gyara a dokar Likitoci da Likitocin Hakora ta kasa, mai lamba ta Cap M379,ta dokokin Nijeriya  shekara ta 2004 domin yin duk wani gyara domin a sa duk wani wanda ya aka horar a matsayin Likitan Hakora ko Likita sai ya yi shekara biyar tukuna kafin a amince ma shi wajen bashi cikakken lasi wanda kungiyar ce zata bada,wannan duk domin a samar da kulawa da lafiyar ‘yan Nijeriya kamar yadda ya dace (HB.2130).

Sai dai kamar yadda ya jaddada Makanjuola cewa yayi “ Hakane shi al’amarin kwararru ta bangaren lafiya yake a kowacce kasar duniya abin ba ya tsaya bane kan Likita,Ko Nas- Nas,da Unguwar-zoma ba,har ma da daukar hotunan wasu cututtuka, da dai sauransu.Duniya tana bukatar kadan daga cikin masu nagarta.

“Babu wanda  zai bari don saboda da kishi kasa kadai zai ki zuwa wurin da za a rika biyan shi har sau goma fiye da abinda ake biyan shi,bayan wannan ma akwai wadansu abubuwa masu bada kwarin gwiwa, sai kuma mutum ya tsaya wurun da ba za a biya shi abinda ya dace ba,wani lokaci abin yayi kasa sosai.Matsalar da muke fuskanta ke nan wannan shi yasa muke ba gwamnati shawara ta kara inganta sharuddan aikin Likitoci da sauran ma’aikatan lafiya,yayin da ta bangaren namu muna yin abinda ya dace na kara  yawan wadanda muke horarwa da yaye su.”

Likitoci
Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Sarakunan Da Suka Yi Wa Turawan Mulkin Mallaka Turjiya A Nijeriya
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Yajin Aiki: Ƙungiyar Likitocin Nijeriya Ta Ba Gwamnati Wa’adin Mako Huɗu

MASU ALAKA

Sana’ar Kilishi:Yadda Ta Bunkasa Daga Jihar Katsina Zuwa Wasu Sassan Nijeriya
Manyan Labarai

Sana’ar Kilishi:Yadda Ta Bunkasa Daga Jihar Katsina Zuwa Wasu Sassan Nijeriya

July 24, 2026
Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare
Manyan Labarai

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 24, 2026
Wasikar Trump Ba Za Ta Taimaki Tinubu Ya Lashe Zaɓen 2027 Ba – ADC
Manyan Labarai

Wasikar Trump Ba Za Ta Taimaki Tinubu Ya Lashe Zaɓen 2027 Ba – ADC

July 23, 2026
Next Post
Har Yanzu Wasa Bai Kare Ba, Cewar Thomas Tuchel

Har Yanzu Wasa Bai Kare Ba, Cewar Thomas Tuchel

LABARAI MASU NASABA

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

July 24, 2026
Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

July 24, 2026
Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

July 24, 2026
An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

July 24, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

July 24, 2026
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

July 24, 2026
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu

July 24, 2026
Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

July 24, 2026
Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

July 24, 2026
Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.