Assalamu alaikum barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na girki adon mata.
Yadda Uwargida za ta hada MASAR DANKALI:
- Sama Da Kasashe 160 Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Sin Tare Da Tsayawa A Bangaren Gaskiya Da Adalci
- Kungiyar NAOWA Ta Nemi Matan Sojoji Su Karfafa Wa Mazajensu Wurin Yaki Da Ta’addanci
Abubuwa da Uwargida za ta tanada sun hada da: Dankalin turawa, Attarugu, Albasa, Magi, Mai, kwai.
Yadda uwargida za ki hada: Za ki samu dankalinki mai kyau ki fere shi ki wanke sai ki nika shi ya yi laushi da kauri kada ki saki ruwa wurin nikan sai in kin jin nikan ya cije sai ki sa ruwan kadan, bayan nan sai ki zube a roba ki yanka albasa ki saka magi da gishiri da kori in kina da dan wani kayan kamshi shima za ki iya sawa ki fasa kwanki kamar biyu haka, sai ki dauko attaruhunki ki wanke shi, ki daka, sai ki zuba daidai yadda ki ke so sai ki dora Tandar wato abin suyar masar ki a wuta ki zuba mai kamar cokali, biyu idan ya yi zafi sai ki dauko kullin nan naki na dankali wanda dama kin hada shi da kayan dandano ki zuba daidai yadda girman kufin masar yake.
Sai ki barshi sai kasan ya soyu ya yi ja sai ki juya idan kika juya ki kaga bai yi ja ba za ki iya mai dashi.
Amma fa a hankali za ki yi abin don kasa ya barbaje saboda ba shin kafa ba ce balantana ya yi karfi bayan nan sai ki duba inda kika juya shi ma idan ya yi ja sai ki kwashe ta.
Shi kenan uwargida kin gama hada masar dankali, a ci dadi lafiya.
Ana cinta da miyar jajjage., Ko ki yi kayatacciyar miyar alayyahunki ki ci da ita.